Zamu Yi Gaskiya Wajen Tattara Kuri'u A Zabe 2023, Hukumar INEC

Zamu Yi Gaskiya Wajen Tattara Kuri'u A Zabe 2023, Hukumar INEC

  • Hukumar INEC ta yi alkawarin cewa ba za tayi rufa-rufa wajen tattara kuri'u a zaben 2023 ba
  • Shugaban hukumar yace yadda akayi a zaben gwamna Osun da na Ekiti, haka za'ayi a 2023
  • Hukumar ta kaddamar da wani shafin yanar gizo inda za'a rika tattara sakamakon zabe daga rumfuna kai tsaye

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta watau INEC a ranar Juma'a ta baiwa yan Najeriya tabbacin cewa za'a haska gaskiya wajen tattara kuri'u a zaben 2023.

Hukumar ta bada tabbacin cewa zata cigaba da daura sakamakon zaben kuri'u daga runfuna zuwa shafin yanar gizon jam'iyyar kamar yadda aka yi a zaben gwamnan Osun da Ekiti.

Ta baiwa yan Najeriya tabaccin cewa ba za'a yi komai a boye ba kuma kowa zai san abinda ke gudana.

Kara karanta wannan

Osinbajo, Lawan, Da Sauran Mutum 20 Da Suka Sayi Fom Din APC Zasu Gana Don Tinubu

INEC Chari
Zamu Yi Gaskiya Wajen Tattara Kuri'u A Zabe 2023, Hukumar INEC
Asali: Getty Images

Shugaba hukumar, Farfesa Mahmood Yakoubu ya bayyana hakan yayin taron kaddamar da rahoton kungiyar fafutukan Yiaga Africa kan zaben gwamnonin Ekiti da Osun, rahoton TheNation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya yi bayanin sakamakon binciken abinda ya faru a zabukan guda biyu.

Yakubu ya samu wakilcin Barista Festus Okoye a taron.

A cewarsa:

"Hukumar za ta cigaba da daura sakamakon zabe tun daga rumfa zuwa shafin yanar gizon INEC. Ba zamu fasa yin hakan ba."

INEC Ta Kwantar da Hankalin Jama'a, Tace Murde Zaben 2023 Ba Zai Yiwu Ba

A wani labarin, hukumar zabe ta kasa watau INEC ta tabbatarwa mutanen Najeriya cewa ba za ta yiwu ayi cuwa-cuwa wajen tattara sakamakon zabe ba.

Daily Trust tace Farfesa Mohammad Kuna ya bayyana haka a wajen wani taro da Kwamitin NPC da cibiyar The Kukah Centre suka shirya a Abuja.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Nuna Yadda Za a Raba Ayyuka Muddin Tinubu Ya Hau Mulki

Janar Abdulsalami Abubakar shi ne shugaban wannan kwamiti na NPC mai kawo zaman lafiya, sai Bishof Mathew Kukah yake jagorantar cibiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida