Da duminsa: ASUU Reshen UNIZIK ta Ayyana Yajin-Aikin Sai Baba ta Gani

Da duminsa: ASUU Reshen UNIZIK ta Ayyana Yajin-Aikin Sai Baba ta Gani

  • Kungiyar malamai masu koyarwa na reshen jami'ar UNIZIK, ta ayyana yajin aikin sai baba ta gani
  • Kamar yadda shugaban kungiyar , Kwamared Stephen Ufoaroh ya bayyana, suna goyon bayan ASUU a kowanne mataki
  • Ya bayyana cewa, ASUU na kokarin ceto jami'o'in gwamnati na kasar nan wacce kashi 95 na 'yan Najeriya ke halarta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Awka - Kungiyar Malamai Masu Koyarwa ta Jami'o'i reshen jami'ar Nnamdi Azikiwe ta snar da shiganta yajin aikin sai baba ta gani bayan amincewar malaman jami'ar.

Vanguard ta ruwaito, bayan taron da suka yi Awka, shugaban kungiyar, Kwamared Stephen Ufoaroh yace UNIZIK yana goyon bayan shugabannin kungiyar na kasa, shiyya da reshen kan yajin aikin.

Yace:

"Sakamakon rashin mayar da hankali kan yarjejeniyarsu da ASUU duk da yajin aikin bayan wata shida, ASUU-NAU ta yanke hukuncin tafiya yajin aikin sai baba ta gani har sai an shawo kan matsalar dake tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Rufe Ofishin NNPP Da Yan Sanda Suka Yi A Borno Gabanin Ziyararsa

“Taron ASUU NAU ta tabbatar da goyon bayanta ga shugabannin kungiyar na reshen kasa da na shiyya wurin kokaron ganin ta ceto jami'o'in gwamnati a Najeriya, inda sama da 95% na daliban Najeriya ke karatu, da kuma zamanta na muryar 'yan Najeriya."

DMO: Zunzurutun Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Zarta Kudin Shiga da Take Samu

A wani labari na daban, Najeriya ta kashe kudade masu yawa wurin biyan bashi fiye da wanda take samu tsakanin watan Janairu zuwa Afirilu na wannan shekarar inda darakta janar na Ofishin Kula da Basusska, Patience Oniha.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yawan kudin da ake amfani da shi wurin biyan bashi ya zama abun damuwa ga gwamnatin tarayya saboda a watanni hudu na farkon shekarar nan ta biya bashi da sama da kudin shigar da take samu.

Kara karanta wannan

Mun ki din: ASUU ta yi martani kan tayin iyayen dalibai na tara musu N10,000

Darakta janar din ta kara da cewa, yawan kudaden da ake biyan bashi ya karu da kashi 109 tsakanin watan Disamban shekarar da ta gabata da na Maris din wannan shekarar, daga N429 biliyan da N896 biliyan.

The Nation ta rahoto cewa, kamar yadda bayanan da ofishin kula da basukan suka bayyana, an kashe N3.83 tiriliyan wurin biyan bashi a kasar nan cikin watanni 15.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng