Gwamnatin Tarayya Ta Raba N20,000 Ga Talakawa Sama Da 3,000 a Taraba

Gwamnatin Tarayya Ta Raba N20,000 Ga Talakawa Sama Da 3,000 a Taraba

  • Gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta fara raba N20,000 tallafi ga talakawa masu ƙaramin karfi a jihar Taraba
  • Ministar jin kai da harkokin walwala, Sadiya Farouk, ta ce sama da mutum 500,000 ne suka ci gajiyar ayyukan jin kai a jihar
  • Ministar ta ce shugaba Buhari ya ba da umarnin ware kaso 70 na mutanen da zasu ci gajiyar tallafin ga mata

Taraba - Gwamnatin tarayya ta fara aikin raba tallafin N20,000 ga mutane masu matsakaicin karfi a jihar Taraba, Arewa maso gabas a Najeriya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ministar jin ƙai da walwalar al'umma, Sadiya Farouq, ita ce ta kaddamar da fara rabon tallafin ga mutane 3,110 da ake sa ran zasu ci gajiyar shirin ranar Alhamis a Jalingo, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Wata Matashiya Da Ta Haihu Da Saurayinta Ta Sayar Da Jaririn Ɗan Mako Uku N600,000

Minista, Sadiya Farouk, tana raba tallafi.
Gwamnatin Tarayya Ta Raba N20,000 Ga Talakawa Sama Da 3,000 a Taraba Hoto: Nasims/facebook
Asali: Facebook

Ta bayyana cewa sama da mutum 500,000 a sassan kananan hukumomi 16 na jihar ne suka amfana daga tallafin jin ƙai kala daban-daban ƙarƙashin shirin NSIP da gwamnatin tarayya ta ɓullo da shi.

Ministar ta jaddada cewa alƙaluma sun nuna jihar Taraba na ɗaya daga cikin jihohin da suke sahun gaba a yawan mutanen da zasu ci gajiyar tallafin N20,000 a faɗin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai ta alaƙanta haka da tasirin ayyukan ƴan ta da ƙayar baya da kuma yawan yan gudun hijira da jihar ke tattare da su.

A jawabinta ta ce:

"Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin cewa kaso 70% na waɗan da zasu ci gajiyar tallafin wajibi su kasance mata, yayin da ragowar 30% aka barwa matasa."
"Shugaban ya kuma umarci cewa kaso 15% na jimullan waɗan da zasu amfana ya tafi ga mutane masu bukata ta musamman, wanda ya haɗa da nakasassu da tsofaffi."

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Kai Samame Haramtacciyar Kasuwar 'Yan Ta'adda, Sun Hallaka Su Da Dama a Arewa

Yayin da take gode wa gwamnan jihar bisa haɗin kan da gwamnatinsa ta bayar, Sadiya, ta ja hankalin gwamnatin ta yi koyi da irin waɗan nan ayyukan da zasu canza rayuwar talakawa.

Gwamna ya yaba wa FG

A ɓangarensa, gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatinsa, Anthony Jellason, ya yaba wa FG wajen tabbatar da ba'a bar masu ƙaramin karfi a baya ba, kamar yadda Sun News ta ruwaito.

A wani labarin kuma Tsohon Shugaban Shirin Sulhun Tarayya, Farfesa Dokubo, Ya Rasu a Abuja

Tsohon shugaban shirin sulhu na gwamnatin tarayya, Farfesa Charles Quaker Dokubo, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya.

Bayanai sun nuna cewa Farfesa Dokubo ya mutu ne a wani Asibiti da ke birnin tarayya Abuja ranar Laraba 24 ga watan Agusta 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262