Katsina: Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari, Sun Sace Matafiya Da Dama
- Yan bindiga, a ranar Laraba sun tare matafiya a hanyar Katsina zuwa Jibiya inda suka kwashe da dama daga cikinsu zuwa wani wurin da ba a sani ba
- Majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 5 na yamma suka rika harbi a titin kafin sace mutane
- Shaidan gani da ido ya yi ikirarin cewa an sanar da jami'an tsaro amma ba su taho ba sai bayan kimanin minti 30 da tafiyar yan bindigan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Katsina - An rahoto cewa wasu yan bindiga sun tare hanyar Katsina zuwa Jibia a ranar Laraba kuma suka sace matafiya da a yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Wani shaidan gani da ido ya ce harin ya faru ne misalin karfe 5 na yammacin kauyen Kadobe, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majiyar ta ce yan bindigan da suka taho kan babura shida, sun mamaye hanyar suka rika harbe-harbe don firgita matafiya sannan suka sace mutanen da ke cikin wasu motocci biyu.
Ya ce:
"Ba su wuce su 20 ba saboda kan babura shida suka taho. Ba su yi amfani wani abu sun tare hanyar ba, kawai sun tsaya kan hanyar ne da bindigu suka fara harbi. Bayan hakan suka kwashe mutanen motocci biyu."
Shaidan ya yi ikirarin cewa an sanar da jami'an tsaro a lokacin da ake harin amma ba su taho ba sai kimanin minti 30 bayan maharan sun tafi.
Daily Trust ta rahoto cewa yan bindiga suna kai hare-hare a hanyar Katsina - Jibia a baya-bayan nan duk da jami'an tsaro da aka zuba a hanyar da barikin soja.
Martanin yan sanda
Ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ba saboda bai daga wayarsa ba.
An Kama Sojoji 2 Kan Laifin Kashe Babban Malamin Islama, Sheikh Goni Aisami, Tare Da Sace Motarsa A Yobe
A wani rahoton, Rundunar yan sandan Najeriya a Yobe ta kama sojoji da ake zargi da hannu a kisar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Goni Aisami wanda aka kashe ranar Juma'a misalin ƙarfe 9 na dare a hanyarsa ta komawa Gashua daga Kano.
Majiyoyi da dama daga garin sunyi zargin cewa sojojin sun kashe malamin ne bayan ya rage musu hanya daga shingen sojoji a Nguru zuwa Jaji-maji, wani gari da ke karamar hukumar Karasuwa na Jihar Yobe.
Majiyoyin sun ce an bindige shi ne har lahira yayin da sojojin suka tafi da motarsa, jar Honda Accord (Discussion Continues) kafin yan sanda suka kama su, Daily Nigerian ta rahoto.
Asali: Legit.ng