Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki Kan Hukunta Sojan Da Ya Kashe Malami a Yobe
- Majalisar Dattawa ta nemi mahukunta su gaggauta daukar mataki kan sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami Gashuwa jihar Yobe
- Shugaban majalisar, Sanata Ahamad Lawan, shi ne ya yi wannan kiran yayin da ya je ta'aziyya gidan marigayin
- Lawan ya kuma yaba wa hukumomin tsaro bisa nasarar da suke samu kan ƴan ta'adda a kwanakin nan
Yobe - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya yi kira da a gaggauta ɗaukar matakin adalci kan kisan Sheikh Goni Aisami Gashuwa a jihar Yobe.
Vanguard ta rahoto cewa Lawan ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Marigayin a garin Gashuwa ranar Laraba.
Sanatan ya bayyana cewa ya je ta'aziyyar ne a karan kansa da kuma a madadin majalisar dattawa. Ya kuma gode Allah bisa kama sojan da ya aikata wannan ɗanyen aiki.
A jawabinsa ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na zo nan ne domin na yi ta'aziyya ta musamman ga iyalan Marigayi Sheikh Baba-Goni Aisami, wanda wani Sojan Najeriya ya yi ajalinsa. Mun gode Allah ya shiga hannu kuma za'a hukunta shi."
"Zan yi amfani da wannan dama na roki hukumomi musamman hukumar yan sanda ta tabbatar an yi wa marigayi Sheikh adalci cikin gaggawa. Ina tabbatar wa al'umma cewa zamu cigaba da bibiyar wannan Kes har sai an yi adalci."
Wane mataki zasu ɗauka domin kare haka a gaba?
Yayin da yake Addu'a Allah ya sa Aljannah ta zamo makomar marigayin, shugaban Sanatocin ya yaba wa mutanen Gashuwa kan yadda suka kwantar da hankulan su da zaman lafiya lokacin da lamarin ya auku.
Ya ce za'a ɗauki duk matakan da suka dace domin kauce wa faruwar haka nan gaba a dukkan sassan ƙasar nan. Channels tv ta rahoto Lawan na cewa:
Hotuna: Dan Maiduguri Ya Kera Adaidaita Mai Aiki Da Lantarki Wanda Ka Iya Gudun 120Km Bayan Chajin Minti 30
"A duk lokacin da zamu ɗauki sabbin Sojoji da sauran hukumomin tsaro, wajibi mu tattara bayanai tare da bin kwakkwafin kowane me neman shiga aikin don tabbatar da bamu ɗauki masu hali mara kyau ko tarihin aikata laifi ba."
Shugaban majalisar dattawan ya yaba wa hukumomin tsaro bisa cigaban da aka samu a ɓangaren tsaron ƙasar nan a baya-bayan nan.
A wani labarin kuma Ba Zamu Yarda Ba, A Gaggauta Hukunta Sojojin Da Suka Kashe Sheikh Aisami, IZALA Ta Yi Martani
Ƙungiyar Izala ta ƙasa ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta hukunta sojojin da suka ƙashe Malaminta a jihar Yobe.
Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce IZALA ba zata yarda irin wannan ta'addancin ba kuma zasu zuba ido su ga matakin da mahukunta zasu ɗauka.
Asali: Legit.ng