Mutum 1 Ya Mutu, 10 Sun Jikkata Sakamakon Arangama Tsakanin Mabiya Addinin Gargajiya da Kiristoci a Legas
- Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta bayyana yadda rikici ya barke tsakanin mabiya addinin kirista da na gargajiya
- An hallaka mutum daya yayin da mutum 10 suka jikkata a arangamar da ta barke tsakanin mabiya addinan
- Ana yawan samun rikice-rikice da tashe-tashen hankula tsakanin mabiya addinai daban-daban a Najeriya
Jihar Legas - Rahoton da ke fitowa daga jihar Legas ya bayyana cewa, mutum daya ya mutu yayin da 10 suka jikkata a wani artabu tsakanin mabiya addinin gargajiya da kirista.
Rundunar 'yan sandan jihar da take tabbatar da faruwar lamarin ta ce hakan ya faru a yankin Oko-Oba na jihar.
Rahotanni sun ce, an kira 'yan sanda a ranar Talata domin sanar dasu ana rikici, ana kokarin kone-kone a wurin da kiristoci ke ibada.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Benjamin Hundeyin, ya yada wannan batu a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana yadda lamarin ya far.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya rubuta cewa:
"Mabiya addinin Oro sun yi arangama da wasu mambobin coci da ke wani sintiri. Hakan ya kai ga mutuwar mutum daya.
"A zahirance lamari ne na kisan kai. An kama wadanda ake zargi da aika-aikan. To amma yanzu, ta yaya za mu tabbatar da juriya tsakanin addinai a irin wannan yanayi?"
Jaridar TheCable ta ce jami'in ya bayyana cewa, har yanzu ana ci gaba da bincike don gano bakin zaren.
Kungiyar CAN Za Ta Fallasa Makarantun da ake Muzgunawa Kiristoci a Najeriya
A wani labarin, kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN ta umarci shugabanninta na jihohi da shiyyoyi da su gabatar da sunayen makarantun da ake muzguna masu.
Jaridar Punch tace kungiyar ta CAN ta na zargin akai wasu makarantun kasar nan da suka maida kiristoci saniyar ware, suke nuna masu bambanci.
Nan gaba kadan CAN za ta saki sunayen wadannan makarantun gaba da sakandare da aka hana kiristoci su gina cocinsu domin su bautawa Ubangiji.
Asali: Legit.ng