Bidiyo: Mai POS ya Fallasa Yadda Za a Iya Kwashewa Mutum Kudi Ba Tare da Saninsa ba
- Wani matashi mai sana'ar POS ya ja kunnen mutane kan yadda zasu gujewa damfara daga masu sana'ar POS
- Kamar yadda yace, za a iya cire kudi hankali kwance daga asusun bankin mutum wanda ya je wurin mai sana'ar POS
- Mutumin kirkin ya bai wa mutane satar amsan yadda zasu gujewa damfara kuma jama'a sun dinga yaba masa kan wannan taimakon
Wan matashi 'dan Najeriya ya samu jinjina da yabo daga jama'a bayan ya basu shawarar yadda zasu gujewa 'yan damfara.
Matashin ya bayyana cewa, yana sana'ar POS ne sama da shekaru biyar kuma za a iya amfani da wannan sana'ar wurin damfarar jama'a
Kamar yadda yace, za a iya satar BVN din mutum yayin da ake cire kudi daga POS, daga nan sai a yi amfani da ita wurin yashe masa asusun bankinsa.
Yadda ake damfarar
Ya shawarci masu amfani da POS da su rike injin cire kudin a hannunsu har sai ya amince da fitar da kudin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan kammala cire kudin, kwastoman ya latsa ja a jikin injin ta yadda bayanin cire kudin da katinsa zai goge da POS din.
Kamar yadda yace, idan ba a yi hakan ba, mai POS din idan 'dan damfara ne zai iya samun BVN kuma ya aike wa manyan 'yan damfara wadanda zasu iya kutse asusun bankin mutum sannan su yashe shi.
"Kada ku yi kuskuren basu katin. Ku tabbatar ba ku basu katin ATM din ba. Kasance tare da katin kuma ka danna ja," ya ja kunne a bidiyon.
'Yan Najeriya sun bayyana tunaninsu
Onestopshop_solutions yace:
"A koda yasuhe akwai zabin tura kudi a maimakon hakan."
Rashida.dee yace:
"A gaskiya wannan bayani ne mai kyau, mun gode da kayi mana shi."
Chuksokonkwoofficial ya rubuta:
"Kati daya nake amfani da shi wurin kasuwanci kuma nake saka kudi a asusun duk lokacin da zan yi amfani da shi."
'Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 6 da Suka Bude Caji Ofis din Bogi Tsawon Wata 8
A wani labari na daban, jami'an 'yan sanda a kasar Indiya sun cafke wasu mutane shida da suka dauka tsawon watannin takwas a matsayin 'yan sandan bogi.
Ba a nan mutum shidan suka tsaya ba, sun bude caji ofis na bogi a wani otal inda suke karbe kudaden mutane hankali kwance, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.
'Yan sandan bogin sun hada baki da wasu maza hudu ne da mata biyu kuma an kama su duk da shugaban wannan damfarar ya arce ba a gan shi ba.
Bayan Shekaru 16 da Aure, Magidanci Ya Fattaki Matarsa, Ya Aure Mai Gidan Haya Don Morar Hayar Kyauta
Asali: Legit.ng