Allah Ya Yi Wa Dan Majalisar Najeriya Rasuwa A Afirka Ta Kudu

Allah Ya Yi Wa Dan Majalisar Najeriya Rasuwa A Afirka Ta Kudu

  • Mutuwa ta sake fada wa kan dan majalisa kuma shugaban masu rinjaye a majalisa dokokin jihar Anambra, Nnamdi Okafor
  • Okafor, wanda ke wakiltar Awka-South 1 a majalisar, ya rasu ne a kasar Afirka ta Kudu a daren ranar Talata 23 ga watan Agusta a cewar rahotanni
  • Ba a riga an tabbatar da sanadin rasuwar dan majalisar ba a har lokacin da aka kammala hada wannan rahoton

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Honarabul Nnamdi Okafor, Shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Anambra ya riga mu gidan gaskiya.

Okafor ya rasu ne a daren ranar Talata a Afirka ta Kudu kamar yadda The Nation ta rahoto.

Dan Majalisar Anambra.
Allah Ya Yi Wa Dan Majalisar Najeriya Rasuwa A Afirka Ta Kudu. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Okafor, dan majalisa wanda ya ke zangonsa na biyu, yana wakiltar mazabar Awka-South 1 a majalisar jihar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: US zata Dawowa Najeriya $23m na Daga Kudin da Abacha ya Handama

Ya shiga majalisar jihar ne a shekarar 2015 a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA).

A halin yanzu babu cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa amma wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce ya yanke jiki ya fadi ne a otel din Sandton City, Johannesburg, Afrika ta Kudu, daga bisani aka tabbatar ya mutu, The Punch ta rahoto.

Kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu ta tabbatar da rasuwar dan majalisar, inda ta ce dan majalisar ya tafi Afirka ta Kudu don wani horaswa ne amma ya rasu awanni kafin dawowa Najeriya.

An Cafke Wani Dan Siyasan Najeriya Mai Karfin Fada A Ji, Yan Sanda Sun Bada Dalili

A wani rahoton, Mbazulike Iloka, dakataccen shugaban kwamitin mika mulki na karamar hukumar Nnewi ta Arewa a Jihar Anambra, ya shiga hannun yan sanda a jihar kan zarginsa da hannu kan mutuwar matarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Allah Ya Yiwa Kauran Katsina Kuma Hakimin Rimi, Nuhu Abdulkadir, Rasuwa

Kakakin yan sandan Jihar, Ikenga Tochukwu, wanda ya yi magana da yan jarida a ranar Laraba 17 ga watan Agusta ya tabbatar da kama Iloka, The Nation ta rahoto.

Tochukwu ya bayyana cewa an kama Iloka ne kan zargin yana da hannu a mutuwarsa, Chidiebere.

Amma, jami'in mai magana da yawun yan sandan ya ce, sashin binciken manyan laifuka na rundunar, SCID, har yanzu tana bincike kan abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164