Zamfara: Kwamitin Yakar 'Yan Bindiga Ya Gindaya wa Turji Sharadin Tuba
- Shugaban kwamitin yaki da 'yan bindiga na jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi, yace sai Turji ya fito ya mika makamansa gaban jama'a ne za a ce ya tuba
- Shinkafi ya tabbatar da cewa, watanni shida da suka gabata farmaki ya ragu amma Bello Turji bai ce ya tuba ba kamar yadda ake hasashe
- Ya jaddada cewa, a matsayinsa ba zai taba zaman neman yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan bindiga ba saboda mayaudara ne kuma marasa gaskiya
Zamfara - Kwamitin jihar Zamfara na gurfanar da laifukan da suka shafi 'yan bindiga sun ce har sai Bello Turji, fitaccen shugaban 'yan bindiga ya fito bainar jama'a ya mika makamansa tare da sanar da tubansa, ba za a karba tubansa a matsayin sahihiya ba.
Shugaban kwamitin, Abdullahi Shinkafi, ya sanar da hakan a jawabin da yayi ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, Channels TV ta ruwaito.
Shinkafi wanda ya fito daga karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda Turji ke yawaita barnarsa, yace kusan watanni shida kenan babu labarin farmakin 'yan ta'adda ko sace mutane da aka saba a yankin da kananan hukumomin Zurmi, Isa da Sabon-Birni.
Daily Trust ta ruwaito cewa, yace rashin farmakin ba yana nufin 'yan bindiga sun daina ta'addancin su bane.
"A abinda na sani, ya rungumi zaman lafiya amma ba zan ce ya tuba ba saboda idan da ya tuba, da ya mika makamansa, ya je wurin gwamnati kamar yadda tubabbun 'yan bindiga ke yi," Shinkafi yace.
Yana martani ne ga sanarwar mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, da yace shugaban 'yan bindigan ya rungumi zaman lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya sha alwashin cewa ba zai sassauta ba kuma ba zai kasance cikin wadanda zasu yi tattaunawar yarjejeniya da kowanne 'dan bindiga ba, inda ya kwatanta lamarin da yaudara.
"Duk wani abu da ya shafi tattaunawa da 'yan bindiga, ku cire ni a ciki saboda da yawansu basu da amana kuma basu da gaskiya. Duk abinda ku ka yarje musu, zasu koma kan mugun halinsu, da yawansu."
Shinkafi ya koka kan tsawon lokacin da ake dauka wurin gurfanarwa tare da hukunta 'yan bindigan da aka kama da masu daukar nauyinsu.
Tuban Turji: 'Yan Najeriya Sun yi Martani, Suna Zargin Akwai Lauje Cikin Nadi
A wani labari na daban, 'yan Najeriya sun dinga martani kan rahoton dake bayyana cewa gagararren 'dan bindiga Bello Turji, wanda ya saba kashewa da garkuwa da jama'a a Sokoto da Zamfara ya tuba.
Idan za a tuna, a watan Disamban 2021, shugaban 'yan bindigan ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Bello Matawalle da Sarkin Shinkafi kan yana so a tsagaita da ruwan wuta.
A yayin jawabi a wani taro a Gusau a ranar Lahadi, mataimakin gwamnan jihar, Hassan Nasiha, ya bayyana cewa Turji ya tuba kuma ya rungumi matakan zaman lafiya na gwamnatin jihar.
Nasiha yace Turji ya tuba kuma hakan ya dawo da zaman lafiya a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi a jihar.
Asali: Legit.ng