Soyayya Na Bi: Matashiyar Da Ta Baro Birni Ta Koma Rayuwa A Unguwar Talakawa Ta Magantu A Bidiyo
- Wata yar Najeriya mai suna Oluwafunmilayo Fatai ta bar rayuwar da take yi a birni sannan ta koma zama da mijinta a unguwar talakawa a Lagas kuma bata danasani kan haka
- Malamar makarantar ta ba Legit TV labarin yadda ta hadu da mijin nata wanda ke zama a unguwar talakawa har suka fara soyayya
- Oluwafunmilayo ta kuma magantu game da martanin yan uwa da abokanta a lokacin da ta yanke shwarar komawa yankin da aka gina a saman ruwa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagas - Oluwafunmilayo Fatai, wata matashiya yar Najeriya ta jefa yan uwa da abokanta cikin halin mamaki lokacin da ta yanke shawarar komawa unguwar matalauta a Lagas don fara rayuwa da mutumin da ta aura a chan.
Tsawon shekaru shida, malamar makarantar bata taba da na sanin barin birni don fara rayuwa da burin ranta ba.
Da farko Oluwafunmilayo bata son mijin nata
A wata hira ta musamman tare da Legit TV, matar wacce ke da yara uku a yanzu ta bayyana cewa ta auri maigidan nata a 2016.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oluwafunmilayo ta ce aikin koyarwa ne ya kaita unguwar da ke saman ruwa. Za ta koyar a nan sannan ta koma birni.
A cikin haka ne mutumin ya lura da ita sannan ya fara neman soyayyarta.
Da farko bata son sa, amma bayan wasu yan nazari da ta yi a kansa sai ta sauya tunaninta.
“Soyayya ce. Yana da ilimi kuma malamin musulunci ne. Nima musulma ce. Don haka, wannan shine abun da nake so a wajen namiji.
“Shi Musulmi ne na hakika, mutum mai ilimi, mai fadar gaskiya kuma baya taba yin karya kuma yana sona. Don haka me nake nema?”
Oluwafunmilayo ta ce masoyanta na baya suna ta yi mata ba a
Malamar makarantar ta bayyana cewa masu sonta na baya suna ta zolayarta a lokacin da suka ji ta tsayar da mutumin da ke zaune a unguwar matalauta.
“Na kan ji babu dadi a baya amma yanzu, hakan ya yi mun.
“Na yarda cewa duk abun da Allah yace za mu zama ko inda za mu kasance, hakan ce za ta kasance.”
Hukuncin Oluwafunmilayo bai yiwa masoyanta dadi ba
Kan martanin yan uwanta a kan zabinta, Oluwafunmilayo ta ce basu ji dadin abun ba kuma basu goyi bayan auren ba.
Matar wacce ta mallaki kwalin SSCE kuma take burin ci gaba da karatunta kamar mijinta ta kara da cewar hatta kawayenta basa ziyartanta saboda haka. Ta ce:
“Yan uwana basu so auren ba. Basu goyi bayansa ba. Su kan zo ganina saboda jini yafi ruwa karfi.
“Hatta kawayena basa kawo mun ziyara kwata-kwata. Kawayena sun zo ne kawai a lokacin da na yi aure.”
Bayan Shekaru 16 da Aure, Magidanci Ya Fattaki Matarsa, Ya Aure Mai Gidan Haya Don Morar Hayar Kyauta
Na Hadu Da Shi Bai Da Ko Waya: Budurwa Ta Kasance Da Saurayinta Har Ya Siya Motar Benz
A wani labarin, wata matashiyar budurwa @barbie_lucienne ta wallafa wani bidiyo da ke nuna saurayinta da ta kasance tare da shi lokacin da bai da komai.
Budurwar ta bayyana cewa a lokacin da ta fara soyayya da shi, mutumin bai da koda wayar hannu. Ya kasance talakan talak.
Bayan bidiyon ya fara tafiya, sai aka gano su tare a cikin wata dankareriyar mota kirar Mercedes Benz yayin da suka rike hannayen junansu cike da so da kauna.
Asali: Legit.ng