Kungiyar Kwadago ta Kasa ta Goyi Bayan ASUU, ta Bullo wa FG da Sabuwar Barazana

Kungiyar Kwadago ta Kasa ta Goyi Bayan ASUU, ta Bullo wa FG da Sabuwar Barazana

  • Kungiyar malamai ta ASUU ta samu gagarumin goyon baya daga takwararta ta kwadago kan cewa da ta yi lallai sai an biya mambobinta albashin watanni shida da suka yi suna yajin aiki
  • NLC ta ce babu kyaytawa idan har gwamnatin tarayya tace ba za ta biya malaman jami'o'in albashinsu ba domin ba sune suka ja yajin aikin yayi tsawo ba
  • Kungiyar kwadagon ta nemi jami'o'in kudi da na gwamnati su hada kai don kawo karshen wannan rikici

Kungiyar kwadago ta kasa a jiya ta goyi bayan kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'in, ASUU, kan jaddadawa da tayi cewa sai an biya mambobinta albashinsu da aka rike na tsawon watanni shida da suka kwashe suna yajin aiki.

Kungiyar tace babu kyautatawa a bayanin gwamnatin tarayya na cewa ba zata biya su albashin watannin ba, wanda ba malaman makarantar bane silar tsawaitar yajin aikin.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Karamar Yarinya Ta Yi Suman Karya Bayan Mahaifiyarta Ta Kama Ta Tana Fentin Bandaki

Asuu da NLC
Kungiyar Kwadago ta Kasa ta Goyi Bayan ASUU, ta Bullo wa FG da Sabuwar Barazana Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

A yayin kira ga gwamnati da ta ajiye makamanta kuma ta kasance mai kyautatawa, NLC ta ja kunne cewa zata iya fadawa yajin aiki a dukkan kasar nan kuma a rufe dukkan jami'o'in dake bude yanzu.

Shugaban fannin yada labarai na NLC, Benson Upah, ya bayyana matsayar kungiyar na cewa dalibai sun roki hadaka tsakanin jami'o'in kudi da na gwamnatin domin kawo karshen rikicin, jaridar The Nation ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, karamin ministan ilimi, Goodkue Opiah, ya shawarci 'yan Najeriya da kada su bar yajin aikin ASUU ya lalata sama da N3 tiriliyan da mulkin shugaba Buhari ya zuba a fannin ilimi.

Ministan ilimi, Adamu Adamu, a makon da ya gabata ya ce matsawar da ASUU tayi na cewa sai an biya mambobinta albashinsu da aka rike shi ke tsayar da sasancinsu.

Kara karanta wannan

Atiku: Sai na mai da jami'o'in tarayya karkashin gwamnatin jiha idan na gaji Buhari a 2023

Ya kara da cewa, gwamnatin ta biya dukkan bukatun ASUU banda biyan malaman albashi, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya ki amincewa.

Bukatar kungiyar ta gaza da samar da kudade domin farfado da jami'o'in, biyan alawus din malaman, biyan albashin da aka rage musu da sauransu.

Upah a wata tattaunawa da The Nation tayi da shi a Abuja, yace gwamnatin ta biya albashin watanni shidan kafin su bude jami'o'in da aka rufe tun ranar 14 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng