“Zan Iya Hada miliyan N10 Duk Wata”: Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ke Mayar Da Sharar Robobi Su Zama Bulo

“Zan Iya Hada miliyan N10 Duk Wata”: Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ke Mayar Da Sharar Robobi Su Zama Bulo

  • Wani matashi dan Najeriya ya ce zai iya tara naira miliyan 10 duk wata daga sana’ar yin bulo idan har ya samu cikakken tallafi
  • Matashin mai suna Promise yana tattara robobi da aka zubar sannan ya mayar da su bulo mai wuyan tsagewa
  • Ya bayyana cewa baya da kudaden da zai siya kayan aikin da ya kamata don bunkasa sana’ar tasa zuwa mataki na gaba

Najeriya - Wani hazikin dan Najeriya ya ce idan har ya samu tallafi yadda ya kamata, zai dunga samun makudan kudade daga aikinsa na yin bulo.

Matashin mai kwazo wanda ake kira da suna Promise yana yin bulo masu kwari wanda ake amfani da su wajen gini da sharar robobi da aka zubar.

Mai yin bulo da robobi
“Zan Iya Hada miliyan N10 Duk Wata”: Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ke Mayar Da Sharar Robobi Su Zama Bulo Hoto: @luckyudu.
Asali: Instagram

Sai dai a cikin wani bidiyo da ya yi, Promise ya ce a yanzu haka bashi da kudaden da zai inganta sana’arsa zuwa matakin samun riba.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Tsoho mai shekaru 66 ya kama tallan mangoro don tara kudin maganin matarsa

Ya ce bashi da kayan aikin da ake bukata don yin bulo din da yawa da kuma yin kasuwancin yadda yake so.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata Baturiya ta tallafa mun da wasu kudade

Promise ya ce ya samu tallafi daga wata mata daga Netherlands wacce ta bude masa asusun neman tallafi.

Ya ce yawan kudin da ake son tarawa a asusun shine Yuro 1000 amma cewa Yuro 160 kawai aka samu wanda tuni aka tura masa amma cewa ba zai isa ba.

Promise ya magantu a wabi bidiyo da @luckyudu ya yada.

Kalli bidiyon a kasa:

Mabiya dandalin Instagram sun yi martani

@iam_estee1 ya ce:

"Wannan ya yi kyau, hanya mafi dacewa na sarrafa shara. Ya kamata a samu karin mutane da za su yi wannan da kuma raba muhallinmu da sharar robobi."

Kara karanta wannan

Shin tana kanne: Martanin 'yan Najeriya ga bidiyon wani matashin da ya yi wuff da baturiya

@phayboi ya yi martani:

“Wannan bidiyo mai daraja ne! Wannan shine bidiyo mafi kyau da na kalla a yau. Ina fatan wannan gayen ya samu dukkan tallafin da yake bukata don ci gaba da aiki. Ina matukar kaunar abin da yake yi. Ina fatan tallafawa wata rana.”

Mustapha Gajibo Ya Kera Motocin Bas Masu Amfani Da Lantarki, Hotunan Sun Kayatar Da Mutane

A wani labarin, yan Najeriya a soshiyal midiya sun cika da murnar ganin sabbin motocin bas masu amfani da lantarki wanda Injiniya Mustapha Gajibo ya kera a Maiduguri.

Gajibo wanda ya kasance sanannen injiniyan makamashi ya wallafa kayatattun hotunan sabbin motocin bas din a shafinsa na Twitter wanda ya burge mutane da dama.

An tattaro cewa sabbin motocin bas din mai cin mutum 12 zai iya gudun kilomita 212 bayan chaji daya tare da shafe tsawon kilomita 110 duk awa daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng