Sunaye: Jihohin Kano, Zamfara da Enugu Sun yi Sabbin Kwamishinonin 'Yan Sanda
- Hedkwatar 'yan sandan Najeriya ta aike da sabbin kwamishinonin 'yan sandan jihohin Kano, Zamfara da Enugu
- A takardar mai lamba TH.5361/FS/FHO/ABJ/SUB.4/715, Lawal Abubakar aka tura Kano, Yusuf Kolo yana Zamfara sai Ahmed Ammani jihar Enugu
- Kamar yadda takardar ta bayyana, sabbin kwamishinonin 'yan sandan zasu fara aiki a take ne bayan fitar takardar
FCT, Abuja - Hedkwatar 'yan sandan Najeriya dake garin Abuja ta tura sabbin kwamishinonin 'yan sanda jihohin Kano, Zamfara da Enugu.
Kamar yadda takardar mai lamba TH.5361/FS/FHO/ABJ/SUB.4/715 ta bayyana, an tura Abubakar Lawal jihar Kano yayin da aka aike Yusuf Kolo jihar Zamfara.
A takardar umarnin, an bayyana cewa Ahmed Ammani ne ya zama sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Enugu.
Wadannan sabbin kwamishinonin 'yan sandan zasu fara aiki a take ne, jaridar Daily Nigerian ta rahoto hakan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, wanda aka dauko daga jihar Enugu, a wani lokacin baya shi ne DPO din yankin Hotoro dake jihar Kano.
Tuban Turji: 'Yan Najeriya Sun yi Martani, Suna Zargin Akwai Lauje Cikin Nadi
A wani labari na daban, 'yan Najeriya sun dinga martani kan rahoton dake bayyana cewa gagararren 'dan bindiga Bello Turji, wanda ya saba kashewa da garkuwa da jama'a a Sokoto da Zamfara ya tuba.
Idan za a tuna, a watan Disamban 2021, shugaban 'yan bindigan ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Bello Matawalle da Sarkin Shinkafi kan yana so a tsagaita da ruwan wuta.
A yayin jawabi a wani taro a Gusau a ranar Lahadi, mataimakin gwamnan jihar, Hassan Nasiha, ya bayyana cewa Turji ya tuba kuma ya rungumi matakan zaman lafiya na gwamnatin jihar.
Nasiha yace Turji ya tuba kuma hakan ya dawo da zaman lafiya a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi a jihar.
Asali: Legit.ng