Yadda 'Yan Bindiga Sun Kallafawa Manoman Kaduna Harajin Miliyoyin Naira

Yadda 'Yan Bindiga Sun Kallafawa Manoman Kaduna Harajin Miliyoyin Naira

  • Manoman Birnin Gwari na jihar Kaduna sun amince da mikawa 'yan bindiga makuden kudade da suka kallafa musu domin zaman lafiya
  • Shugaban BEPU, Ishaq Usman Kasai, yace sun yi yarjejeniya da 'yan bindigan cewa zasu dinga nomansu ba tare da hari ko garkuwa da su ba
  • Hakazalika, 'yan bindigan suna da damar shiga gari su samu cibiyoyin kiwon lafiya, siye da siyarwa tare da sauransu kasuwancinsu

Birnin Gwari, Kaduna - Manoman karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna sun amince zasu biya makuden kudaden da 'yan bindiga suka kallafa musu in har suna son amfani da gonakinsu.

Kamar yadda Ishaq Usman Kasai, shugaban kungiyar masarautar Birnin Gwari, yace 'yan bindigan sun kallafa musu harajin miliyoyin naira kan manoman, Daily Trust ta ruwaito.

Manoman Kaduna
Yadda 'Yan Bindiga Sun Kallafawa Manoman Kaduna Harajin Miliyoyin Naira. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wata takarda, yace manoman sun sun yanke hukuncin yin ciniki da 'yan bindigan saboda basu da wata mafita.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun tarfa jigon APC a yankinsu, sun hallakashi

Yace noma a yankin ya gurgunce a Birnin Gwari da sama da kashi saba'in na yadda suka saba a lokacin da suke iya zuwa gonakinsu a shekaru uku da suka gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A wasu yankuna, manoman sun biya miliyoyin naira kafin a bar su zuwa gonakinsu."
"Wasu daga cikin yarjejeniyar da aka yi a bangaren manoma sun hada da barin manoma su je gonakinsu ba tare da yin garkuwa da su ba ko wani nau'in tsoratarwa daga 'yan bindigan.
"Su kuma 'yan bindiga za a bar su su dinga zuwa birane da kauyuka inda aka yi yarjejeniyar zaman lafiya inda zasu iya samu wuraren kiwon lafiya, siye da siyarwa tare da sauran kasuwanci," yace.

Ya yi bayanin cewa yarjejeiniya ta bar manoman da 'yan bindiga suka kora daga yankunansu kamar Katakaki, Ganda, Mashigi, Ginsa, Biskin, Layin Mai- Gwari, Kwasa-Kwasa da sauran yankunan duk su dinga zuwa gonakinsu.

Kara karanta wannan

Zamu Dira Kan Barayin Man Fetur A Neja-Delta, Shugaba Buhari

BEPU ta kara da cewa, 'yan bindiga masu yawa sun da gonaki a yankunan inda ya kara da cewa fitaccen shugaban 'yan bindiga Dogo Kachalla Gide, yana da gonaki a yankin Mashigi.

Kasai yace 'yan bindigan sun dakatar da garkuwa da mutane da hare-hare a wasu yankunan amma sun cigaba da kwace babura da sauran kadarorin manoman.

Yayi kira ga gwamnatin jihar da ta rungumi duk wani mataki da ta ga ya dace wurin hana 'yan bindigan shugabancin Birnin-Gwari da kewaye.

Rashin Tsaro: Manoman Zamfara Zasu Yi Zaman Sasanci da 'Yan Bindiga

A wani labari na daban, manoma a jihar Zamfara sun shirya ganawa da shugabannin 'yan bindiga a jihar domin sasantawa kan kariya da barinsu su yi noma a gonakinsu.

Idan za a tuna, manoma da mazauna wasu yankuna a jihohin arewa sun ce suna biyan haraji ga 'yan bindiga domin gujewa farmakinsu, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Manoman wadanda suka yi magana karkashin inuwar Kungiyar Manoman Najeriya, reshen jihar Zamfara, sun ce zasu gana da 'yan bindigan a yau Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng