Hoton Yarinya ‘Yar Shekara 5 Dake Burin Zama Jami’ar Yan Sanda, Yan Najeriya Sun Yi Martani

Hoton Yarinya ‘Yar Shekara 5 Dake Burin Zama Jami’ar Yan Sanda, Yan Najeriya Sun Yi Martani

  • Hoton wata karamar yarinya mai suna Lawal Mazeedatul Khair Adesuwa, ya haifar da martani masu yawan gaske a Twitter yayin da ta yi shiga kamar yar sanda
  • Prince Olumuyiwa Adejobi wanda ya wallafa hotunan yarinyar ya bayyana cewa Adesuwa na burin zama yar sanda a rayuwa
  • Hoton yarinyar ya sa mutane da dama shakku kan ko yarinyar za ta ci gaba a kan wannan mafarki nata idan ta girma

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Abuja, Prince Olumuyiwa Adejobi, ya wallafa hotunan wata karamar yarinya, Lawal Mazeedatul Khair Adesuwa, wacce ke son zama yar sanda a rayuwarta.

Olumuyiwa ya bayyana cewa yarinyar na 'Nursery 2'. Ya yi alkawarin sanya idanu a kan ci gaban Adesuwa yayin da yake mata fatan alkhairi.

Yan sanda
Hoton Yarinya ‘Yar Shekara 5 Dake Burin Zama Jami’ar Yan Sanda, Yan Najeriya Sun Yi Martani Hoto: @Princemoye
Asali: Twitter

Jami’ar yar sandan gobe

Kara karanta wannan

Nakuda Mai Tsada: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da

Yarinyar mai shekaru 5 ta yi shiga irin na yar sanda a wani taro da suka yi a makarantansu inda kowani dalibi ya sanya kaya irin na abun da yake burin zama a rayuwa. An bayyana ta a matsayin yarinya mai kwazo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

PRO Olumuyiwa ya ce:

“A ranar nuna abun da take burin zama a makaranta, ta yi shiga a matsayin jami’ar yar sanda cike da tsafta, a zahirib gaskiya, tana burin zama jami’ar yan sanda a koda yaushe. Ina yi mata fatan alkhairi. Zan sanya ido har zuwa girmanta da nasarorin da za ta samu a rayuwa...”

Kalli wallafarsa a kasa:

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin martanin mutane a kasa:

O ya ce:

"Za ta girma sannan ta gane kuskurenta.

@yungs_official ya ce:

"Lol. Ko shakka babu wani a cikin yan uwanta ko makwabta babban jami'in dan sanda ne. Babu dan da zai so ya zama irin mutumin da ke tsare mahaifinsa a kan hanya da kuma bata masu lokaci saboda ba a basa na goro ba, ko mutumin da ke cin zarafi, tsoratarwa da kuma tatse yayanta ko kawunta da tafi so."

Kara karanta wannan

Dan kasuwa ya toshe al'aurarsa saboda bai san ya sake haihuwa saboda tsadar kudin makaranta 'yayansa 5

@dejavu213ta ce: "

"Ina ma ace haka suke da tsafta da yin murmushi kamar wannan yarinyar."

@LoadedDanny ya ce:

"Lokacin da a zama cikakkiyar yan sanda. Sannan ta ga ainahin hoton. Ita da kanta za ta yi murabus."

Ayyiriri: Kyawawan Hotunan Jami’an Yan Sandan Najeriya Yayin Da Suka Shiga Daga Ciki

A wani labarin, mabiya shafukan soshiyal midiya sun taya wasu jami’an yan sandan Najeriya biyu murna yayin da suka shiga daga ciki.

Labaran masoyan ya yadu ne a shafukan soshiyal midiya bayan amaryar ta je shafinta na TikTok don baje kolin hotunansu.

Ta wallafa hotunansu iri-iri dauke da bayanin kowani lokaci a tafiyar soyayyarsu, ciki harda wani bidiyonsu sanye da kayan yan sanda yayin da suka je hirar aurensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng