Kudin Haya 2.7m duk shekara, Kudin Diesel N80k: Bidiyon Gidan Mai Dakuna 3 Da Budurwa Ta Gani A Lagas
- Wata matashiya, Anagu Nkemjika, ta nunawa jama’a gidan haya mai dakuna uku a jihar Lagas da tsayayyen wutar lantarki da ake biyan naira miliyan 2.7
- Matashiyar budurwar tace duk da cewar tana son karbar gidan, dillalin yace masu daukan albashi kawai za su ba haya
- Baya ga kudin hayar, mutum zai dunga biyan N80,000 na man diesel duk wata da karin N600,000 na hidindimu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagas - Wata matashiya yar Najeriya, Anagu Nkemjika, wacce ke neman gidan haya a jihar Lagas ta wallafa bidiyon yawon da ta sha wajen neman gida.
Nkemjika ta bayyana cewa a karshe ta ga irin gidan da take nema kuma kudin hayar gidan duk shekara naira miliyan 2.7 ne kuma yana dauke da dakuna uku.

Asali: UGC
Yan albashi kawai muke so
Ba iya nan abun ya tsaya ba, kudin hayar baya kunshe da kudaden hidindimu N600,000 da kudin man diesel N80,000 duk wata.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Matashiyar ta cika da farin ciki a lokacin da aka bata fom don ta cike a matsayin mai karbar haya sai dai kuma murna ta koma ciki lokacin da suka yi watsi da bukatarta na karbar gidan saboda ita yar kasuwa ce. A cewarta, yan albashi kawai suke so.
Kalli bidiyon a kasa:
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:
Anwan Abasiubong ya ce:
“Miliyan 2.7, hukumar da ake biyan 540k, 80k duk wata gaba daya jimillar miliyan 4.2 kenan a shekara. Akalla 12k kenan a kullun. Ba kayan daki. Nawa ne dakin otel?"
Plantboyng ya ce:
"lol ta yaya kuke sa rana mai cin albashi zai karbi gida a irin wannan farashi mai ban tsoro? Gidan na da ka'ida kuma farshinsa yayi yawa. Tagogin sun yi kankanta, Kin cancanci fiye da haka."

Kara karanta wannan
Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma
Darlington Peters ya ce:
"wato bayan na biya kudin gidan sai kuma kudi kan kudi duk wata. baku fadi a ina kuke samun kudi ba."
042viktorchiya ce:
"miliyan 2.7 zai gina mun nawa gidan."
Abuja Ba Na Yaku-bayi Bane: Budurwa Ta Nuna Gidan Haya Na N750,000 Da Wani Dillali Ya Kaita, Bidiyon Ya Yadu
A wani labari makamancin wannan, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya, Tobi Oduns, ta shafe tsawon lokaci yanzu tana neman gidan haya a Abuja.
Budurwar wacce ke amfani da shafin TikTok tana ta yiwa mabiyanta a manhajar karin bayani game da yadda take faman neman gidan haya.
Kwanan nan ne wani dillalin gida ya dauke ta ya kaita wani gida mai daki daya wanda za a bayar da hayarsa kan N750,000 a babbar birnin tarayyar amma ko kadan bai burgeta ba.
Asali: Legit.ng