'Yan Bindiga Sun Sace Wasu Jiga-Jigan Jam’iyyar APC a Jihar Imo
- Wani rahoto ya bayyana cewa, an sace wasu jiga-jigan APC a jihar Imo, sun hallaka mutane uku a mummunan harin
- An ce hakan ya haifar da hargitsi, masu ababen hawa sun sauya hanya bayan samun mummunan cunkoso
- A cikin makon nan ne aka samu labarin cewa, wasu tsageru sun farmaki ayarin motocin uwar gidan gwamnan Osun
Jihar Imo - A jiya Asabar 20 ga watan Agusta ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC biyu tare da kashe wasu mutum uku a jihar Imo.
Rahoton da muka samo daga jaridar Daily Trust ya ce tsagerun sun mamaye wani sahshe sashe ne na Amaraku-Orji, kan sabuwar hanyar Owerri zuwa Okigwe da aka gyara kwanan nan, kuma sun shafe wani adadi na sa’o’i suna cin karen ba babbaka.
Rahoton ya ce, an sace Mr Aloy Onuekwusi, wanda aka ce shi ne mai Diamond Pools a jihar ta Imo.
Hakazalika, an kashe wani wani mutum da aka ce direban wanda aka ruwaito direba ne ga daya daga cikin jiga-jigan na APC da aka sace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani shaidan gani da ido ya ce lamarin ya haifar da hargitsi, har ta kai ga an samu cunkoson ababen hawa da ya tilastawa masu ababen hawa sauya hanya.
Ya zuwa yanzu, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Imo ba, CSP Mike Abattam.
Wani rahoton jaridar Daily Sun ya ce, Cif Godson Obijiaku ne daya daga cikin biyu da aka sace, yayin da dayan kuma da ba bayyana ainihin sunansa ba aka ce ana kirnansa da 'Ability'.
'Yan Sanda Sun Cafke Mutum 5 da Ake Zargin Sun Farmaki Tawagar Uwar Gidan Gwamnan Osun
A wani labarin, jaridar The Nation ta ruwaito cewa, rundunar an kame wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a farmakar tawagar uwar gidan gwamnan Osun.
A yau Asabar 20 ga watan Agusta ne rundunar 'yan sandan jihar Osun ta tabbatar da an kai farmaki kan ayarin motocin uwar gidan gwamnan jihar, Misis Kafayat Oyetola a jiya Juma'a a Owode na yankin Ede.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar dauke da sa hannun mai magana da yawunta, SP Yesimi Opalola ta bayyana cewa, jami'in tsaro daya ya raunata a harin.
Asali: Legit.ng