Kwarya Tabi Kwarya: Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Aminu Tajuddeen Dantata Da Aisha Bello Dambazau
- Aisha Dambazau, kyakkyawar diyar tsohon ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya, ta shiga daga ciki
- An kulla aure tsakanin Aisha da burin ranta Aminu Tajuddeen Dantata wanda ya kasance jika a wajen Alhaji Aminu Dantata a ranar Asabar, 20 ga watan Agusta
- Tuni bidiyoyin liyafar Dinan bikin suka yadu a soshiyal midiya inda ango da amarya suka yi shiga ta alfarma
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Tsohon ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya, ya aurar da zukekiyar diyarsa, Aisha Dambazau.
An daura auren Aisha da kyakkyawan angonta, Aminu Tajuddeen Dantata a ranar Asabar, 20 ga watan Agusta, a masallacin Al-Furqan da ke Alu Avenue, Nasarawa, jihar Kano.
Tajudden ya kasance jika a wajen shahararren dan kasuwan nan na Najeriya, Alhaji Aminu Dantata.
Duk a cikin shagalin bikin, an gudanar da wani kasaitaccen liyafar Dina inda amarya da ango suka fito shar dasu cikin shiga ta alfarma.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A daya daga cikin bidiyoyin wanda shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram, an gano uwar amarya, Hajiya Hadiza Ado Bayero Dambazau tare da kawayenta a yayin da suka shigo dakin taron. Uwargidar shugaban hafsan sojin kasar ma ta halarci taron.
Kalli bidiyoyin bikin a kasa:
Jama'a sun yi martani
ayish.sani ta yi martani:
"Gaskiya iyayenmu munyi ma kanmu fada wannan Bai dace ba ga Al umma Annabinmu saw ba Allah ka ganar damu gaskiya."
mustaphaahmed941 ya yi martani:
"Na tayaku murna ."
Ba’a Kyauta Mana Mu Talakawa: Rukayya Dawayya ta Koka Kan Yadda ‘Ya’yan Masu Kudi Ke Auran Junansu A Kasar
A wani labarin, shahararriyar jarumar Kannywood, Rukayya Umar Dawayya ta yi martani a kan yadda ake yin kwarya tabi kwarya wajen kulla auratayya a kasar nan.
Dawayya ta shawarci ‘ya’yan talakawa da ke da kyau a kan su daina yarda da soyayya tsakaninsu da yaran masu kudi domin magana ta gaskiya ba auransu za su yi ba.
A cewarta koda yaran na son su iyayensu ba za su amince a kawo masu diyar talakawa a matsayin suruka ba, don haka ta shawarce su da su tashi su nemi ilimi don gobensu.
Asali: Legit.ng