Yan Sanda Sama da 1,000 Sun Yi Zanga-Zangan Kan Rashin Biyansu Albashi a Kwara
- Kuratan yan sanda a jihar Kwara sun gudanar da zanga-zanga kan rashin biyan su Albashi tsawon watanni 16
- Yayin zanga-zangar su, yan sandan sun mamaye muhimman wurare ciki har da titin zuwa fadar gwamnatin jiha
- Hukumar yan sandan Kwara ta bayyana cewa an ɗauki jami'an aiki ne da nufin tsarin jami'an tsaron yanki
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kwara - Aƙallla jami'an hukumar yan sanda 1,056 ne suka fito zanga-zanga kan rashin biyan su Albashi na tsawon watanni 16 da gwamnatin jihar Kwara ta rike musu.
The Nation ta ruwaito cewa Yan sandan sun mamaye muhimman wurare yayin zang-zangar, wanda suka haɗa da Challenge, Post Office da Titin Ahmadu Bello wanda ke zuwa har gidan gwamnati.
Yayin zanga-zangar kuratan yan sandan, sun rinka rera, "Gwamnatin jihar Kwara, a biya mu Albashin mu na watanni 16."
Wasu daga cikin masu zanga-zanga sun hau kan Babura tare da goyon mutum uku yayin wasu suka sanya baƙaƙen kayan yan sanda tare da lulluɓin ganyaye suka mamaye Titunan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Masu zanga-zangar sun yi ƙorafin cewa gwamnatin jiha ba ta biya su albashin su ba tun bayan kammala ɗaukar horon su a watan Afrilu, 2021.
Da take martani kan lamarin, hukumar yan sanda reshen jihar Kwara ta ce am ɗauki kuratan yan sandan ne domin su yi aiki a matsayin jami'an tsaron yanki.
Hotunan Zanga-zangar yan sanda a Kwara
A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun tare matafiya, sun tattara sun yi awon gaba da su a jihar Kwara
Miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane Shida a kan hanyar Obbo-Ile/Osi, a ƙaramar hukumar Eikiti a jihar Kwara yayin da suke kan hanyar koma wa gida daga tafiya.
Daily Trust ta rahoto cewa mutanen da aka sace na kan hanya na cikin wata motar Bas Toyota Hiace bus (Hummer) mai lambar rijista Abuja KUJ 613 AA yayin da tsautsayin ya rutsa da su.
Asali: Legit.ng