SSANU Da NASU Sun Janye Yajin Aiki, Amma Sun Saka Wa Gwamnatin Tarayya Sharadi
- Kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya SSANU da kungiyar ma'aikatan jami'o'i NASU sun dakatar da yajin aikin da suka tafi na watanni
- Mohammed Haruna Ibrahim, shugaban SSANU ya ce sun dakatar da yajin aikin na kawai na kwana 30 don bawa gwamnati lokaci ta cika musu alkawurran da suka dauka
- Kwamared Ibrahim ya ce za su koma yajin aikin idan har wa'adin kwana 6o din ya cika kuma gwamnatin tarayyar bata cika dukkan alkawurran da ta dauka musu ba
Kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya, SSANU da na kungiyar ma’aikatan jami’o’i NASU, a ranar Asabar, sun dakatar da yajin aikinsu bayan gajeren zama da suka yi da ministan Ilimi, Adamu Adamu a Abuja.
Ana sa ran janyewar zai fara aiki ne daga ranar Laraba na mako mai zuwa, Channels TV ta rahoto.
A cewar ministan ilimin, gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 50 don biyan allawus na mambobin SSANU da NASU da na Kungiyar ASUU.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mun dakatar da yajin aikin na kawai na kwana 60, In Ji Kwamared Ibrahim
A hirar da ya yi da wakilin Daily Trust a ranar Asabar, Shugaban SSANU, Kwamared Mohammed Haruna Ibrahim, ya ce an dakatar da yajin aikin na wata buyu.
Ya ce kungiyar ta dauki matakin ne domin bawa gwamnatin tarayya damar aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma.
"Mun janye yajin aikin ne kawai na kwana 60. Wannan kawai dama ce muka bawa gwamnatin tarayya ta cika yarjejeniyar da muka yi da ita. Za mu koma yajin aikin idan gwamnati ta gaza cika alkawarin bayan kwana 60," Kwamared Ibrahim ya ce.
Ya ce dakatar da yajin aikin zai fara aiki ne a ranar Laraba 24 ga watan Laraba.
Wata mamba na NASU ta bayyana ra'ayinta kan daktar da yajin aiki
Legit Hausa ta tattauna da wata babban ma'aikaciyar jinya da ke aiki a asibitin jami'ar ABU Zaria.
Ma'aikaciyar wacce ta bukaci a kada a kama sunanta ta ce ta ji dadin janye yajin aikin saboda mawuyacin hali da ta shiga yayin yajin aikin sai dai ta nuna fargabar cewa ba dole bane gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka musu.
Ta ce:
"Yajin aikin kullin minti ya mana, miji na ma'aikaci ne a jami'a kuma mamba na SSANU, 'ya ta da mijinta suma ma'aikatan jami'a ne don haka abin ya taru ya mana yawa.
"Fata na kawai shine gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka ta yadda ba za a sake komawa yajin aikin ba bayan kwana 60."
Ma'aikaciyar jinyar ta ce tafi wurin aiki a ranar Laraba kuma ta ga masu shara da ban ruwa ga furai sun shigo suna ta aiki.
Asali: Legit.ng