Fitacciyar Jami'ar Kaduna Ta Canja Matsuguni Bayan Yan Bindiga Kashe Mata Dalibai 5

Fitacciyar Jami'ar Kaduna Ta Canja Matsuguni Bayan Yan Bindiga Kashe Mata Dalibai 5

  • Jami'ar Greenfield da ke Jihar Kaduna ta taso dalibanta daga matsuguninta na dindindin ta dawo cikin garin Kaduna
  • Hakan na zuwa ne bayan da yan bindiga suka sace dalibai da malamai daga jami'ar kuma guda biyar suka mutu a hannunsu
  • Shugaban Jami'ar, Farfesa Simon Daniel Katung ya ce jami'ar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin tsare rayyuka da dukiyoyin dalibanta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Jami'ar Greenfield da ke Kaduna ta koma matsuguninta na cikin birnin Kaduna bayan yan bindiga sun kai hari a harabar makarantan na dindindin da ke babban hanyar Kaduna zuwa Abuja a watan Afrilun 2021, Daily Trust ta rahoto.

Kimamin dalibai da malamai 23 ne aka sace yayin harin da yan bindigan suka kai yayin da dalibai biyar suka mutu a hannun yan bindigan.

Kara karanta wannan

'Zan Fitar Da Najeriya Daga Duhu', Atiku Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Bangaren Lantarki

Jami'ar Greenfield.
Jami'ar Kaduna Ta Canja Matsuguni Bayan Yan Bindiga Kashe Mata Dalibai 5. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jami'ar, Farfesa Simon Daniel Katung yayin bikin daukan dalibai karo na 4 ya gargadi dalibansa su dena wallafa bayanai game da makarantar da soshiyal midiya.

Ya bukaci daliban su rika takatsantsan da tsaronsu sannan su dena tafiye-tafiyen dare, kamar yadda The Guardian ta rahoto.

Ya tabbatarwa daliban yara cewa makarantun a shirye ta ke don yaye dalibai da za su iya gogayya da takwarorinsu na kasashen duniya.

Shugaban Jami'ar ya gargadi dalibai game da yawon dare da kungiyar asiri

Katung ya yi gargadin cewa makarantar ba za ta amince da ayyukan kungiyar asiri ba yana mai cewa nan take za a kori duk wanda aka samu da aikata hakan.

"Jami'ar za ta cigaba da aiki tukuru don tabbatar da tsaron rayyuka da dukiyoyin dalibai. Amma ana bukatar daliban su rika kiyaye matakan tsaro yayin da suke makaranta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Lakcara Ta Taya Dalibarta Rainon Jinjirinta Yayin da Take Rubuta Jarrabawa

"Ana shawartar daliban su rika dawowa makaranta da wuri, domin ba za a amince da yawon dare ba," in ji shi.

Ya ce yanzu zamani ne na soshiyal midiya amma ya bukaci su rika amfani da kafar don aikata abubuwa masu amfani ga jami'ar.

A cewarsa, ba a tsammin dalibai su wallafa wani abu game da jami'ar ba tare da neman izini daga shugaban makarantar ba ta hannun jami'in kula da dalibai.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164