Bidiyon Yadda Lakcara Ta Taya Dalibarta Rainon Jinjirinta Yayin da Take Rubuta Jarrabawa
- Wata lakcara ta yi abun azo a gani ta hanyar taya dalibarta da ke rubuta jarrabawa rainon jinjirinta
- Lakcarar wacce ita ce ke sanya idanu kan gudanarwar jarrabawar ta dauki ragamar kula da jarinrin don mahaifiyarsa ta samu sararin yin rubutu yadda ya kamata
- Bidiyon faruwar lamarin ya ja hankalin masu amfani da TikTok inda suka jinjinawa wannan karamci na malamar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wata lakcara da ke sanya idanu kan yadda ake gudanar da jarrabawa ta nuna karamci sosai bayan ta taya wata dalibarta da ke zana jarrabawa kula da jinjirinta.
A cikin wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano lakcarar tana rainon jinjirin dalibar tata cikin yanayi mai ban tausayi.
An kira ta da dadadan sunaye a yanar gizo
A cikin dan gajeren bidiyon wanda aka daura a TikTok, an gano lackarar tana zagaye dakin jarrabawar dauke da jinjirin a hannunta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ta raini jinjirin kamar yadda uwarsa za ta yi, kuma masu amfani da TikTok sun bayyana lamarin a matsayin mai taba zuciya.
Dan gajeren rubutu da aka yi kan bidiyon ya ce:
“Wata lakcara tana aiwatar da aikin dalibarta a matsayin uwa yayin da take rubuta jarrabawa. Allah ya albarkaci matar.”
Wasu mabiya shafukan soshiyal midiya sun ce sun san matar da ake magana a kai kuma sun tabbatar da cewa tana da kirki sosai.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
@marisky360 ta ce:
“Ina son ta. Mutuniyar kirki ce. A kodayaushe tana yiwa mutane alkhairi.”
@Priscy_baibe ta yi martani:
“Allah ya yi maki albarka.”
@user1363677956918 ya ce:
“Allah ya yi maki albarka sosai.”
@mariamsakibu ta yi martani:
“Sannu da kokari aiki ya yi kyau Allah ya yi maki albarka.”
Iyaye Sun Je Bikin Yaye Dansu Daga Jami’a, Sun Sume Bayan Sun Gano A Aji 2 Yake Har Yanzu
A wani labarin kuma, wata wallafa da 3news.com ya yi ya bayar da labarin wasu iyaye da suka sume bayan sun gano cewa dansu da ya kamata ace ya kammala makaranta yana nan a shekara ta biyu.
A cewar rahoton, iyayen sun sume a yayin bikin yaye daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta Kwame Nkrumah a ofishin mai kula da harkokin dalibai.
Jami’in hulda da jama’a na jami’ar KNUST, Dr Norris Bekoe, ya karfafawa iyaye gwiwa a kan su dunga neman hujjar biyan kudin makaranta daga wajen yaransu.
Asali: Legit.ng