Iyaye Sun Je Bikin Yaye Dansu Daga Jami’a, Sun Sume Bayan Sun Gano A Aji 2 Yake Har Yanzu

Iyaye Sun Je Bikin Yaye Dansu Daga Jami’a, Sun Sume Bayan Sun Gano A Aji 2 Yake Har Yanzu

  • Dr Norris Bekoe, jami’in hulda da jama’a a jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah, Ghana ya bayyana yadda wani dalibi ya sumar da iyayensa saboda kaduwa
  • Jami’in KNUST ya bayyana cewa iyayen yaron sun zo makarantar don bikin yaye dan nasu kawai sai suka gano har yanzu a shekara ta biyu yake a jami’ar
  • Dr Bekoe ya bukaci iyaye da ke da yara a jami’ar da su dunga tabbatar da ganin cewa sun samu hujja na biyan kudin makaranta daga yaransu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata wallafa da 3news.com ya yi ya bayar da labarin wasu iyaye da suka sume bayan sun gano cewa dansu da ya kamata ace ya kammala makaranta yana nan a shekara ta biyu.

A cewar rahoton, iyayen sun sume a yayin bikin yaye daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta Kwame Nkrumah a ofishin mai kula da harkokin dalibai.

Kara karanta wannan

Daga Tallar Gwanjo Zuwa Miloniya: Bidiyon Matashi Usman Da Allah Yayi wa Daukakar Dare Daya

Mace da dalibai
Iyaye Sun Je Bikin Yaye Dansu Daga Jami’a, Sun Sume Bayan Sun Gano A Aji 2 Yake Har Yanzu Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar KNUST, Dr Norris Bekoe, ya karfafawa iyaye gwiwa a kan su dunga neman hujjar biyan kudin makaranta daga wajen yaransu.

Ya kuma bukaci iyaye da su dunga bincikar kokarin yaransu a bangaren karatu da kuma halayyarsu a makaranta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ga jawabinsa a kasa

Dr Norris Bekoe ya bayyana cewa akwai daliban da basa mayar da hankali sosai kan karatunsu, wanda shine babban dalilin da yasa aka turo su makaranta. Sakamakon haka, basu samu adadin makin da ake so mutum ya samu ba kafin ya kara gaba.

Idan hakan ya faru, ana tilasta masu neman sabon gurbin karatu sannan su fara daga farko a wasu lokutan, ba tare da sanin iyayensu ba, 3news.com ya rahoto.

Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Ya Gano 'Yar TikTok Ta Yi Amfani Da Hotonsa Matsayin Marigayin Kawunta

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

A wani labarin kuma, wani matashin dan Najeriya mai suna Chima ya cika da mamaki bayan ya gano cewa wata ‘yar TikTok ta yi amfani da hotunansa a shafinta, inda ta yi ikirarin cewa shi din kawunta ne da ya mutu kwanan nan.

‘Yar TikTok din ta yi amfani da hotunan Chima wajen tsara wani bidiyo dauke da rubutun da ke nuna cewa shi din ya mutu.

Matashin ya je shafinsa na Twitter domin nuna takaicinsa a kan wannan abu da ‘yar TikTok din ta yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel