Bidiyo: Babu Dabara Ka Narka Kudinka Ka Gina Gida, Matashi Ya Shawarci Masu Saka Hannayen Jari

Bidiyo: Babu Dabara Ka Narka Kudinka Ka Gina Gida, Matashi Ya Shawarci Masu Saka Hannayen Jari

  • Nguea Dipita, wani matashi ya bayyanawa jama'a yadda yafi dacewa su yi amfani da kudinsu, ya shawarcesu da su gujewa gina gidaje ba tare da suna da wasu hanyoyin samun kudi ba
  • Dipita ya kara da cewa, mutanen da basu da tsarin yadda zasu kashe kudadensu yadda ya dace ne suke karewa a abubuwan da ke cigaba da kwashe kudaden
  • Jama'a da yawa a soshiyal midiya sun yi martani kan wannan ra'ayin inda wasu basu yarda da abunda yace ba na zuba hannayen jari a bangaren gina gidaje

Wani mutum mai sun Nguea Dipita a TikTok ya shawarci jama'a da su guji zuba hannayen jarinsu wurin gidan gidaje inda yace kara lashe musu kudi kawai suke yi.

Ya fara koyarwarsa ne ta hanyar magana kan gidajen da aka gina aka bari a yankin da yake kuma yace masu shi suna ginin tun yana makarantar firamare.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Matashi Yayi Ido Biyu da Mahaifinsa Yana Kama Dakin Otal da Wata Mata

Matashi
Bidiyo: Babu Dabara Ka Narka Kudinka Ka Gina Gida, Matashi Ya Shawarci Masu Saka Hannayen Jari. Hoto daga TikTok/@dr_nguea_dipita
Asali: UGC

Ku habaka yawan kudaden da zasu dinga shigo muku

Dipita yace har zuwa yanzu, mutumin bai kammala ginin ba inda yace babban kuskuren da mutane ke yi shi ne saka kudinsu inda zasu tsaya cak da sunan gina gidaje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa, abinda mutum zai yi idan yana son ya dinga samun kudin shiga shine ya zuba hannayen jarin a wuraren dake kawo kudi tsagwaro.

Kalla bidiyon a kasa:

Martanin jama'a

Wannan bidiyon ya dauka hankalin jama'a inda suka dinga tofa albarkacin bakunansu kan wannan ra'ayin matashin. Ga wasu daga cikin tsokacin:

Dale carnage:

"Ya faru a kaina a 2011, na kara da siyar da gidan amma har yanzu ina tunanin wannan kuskuren da na tafka."

Zen:

"A saka kudaden a ina kenan? Wannan shi ne babbar matsalar."

Kenkutie:

Kara karanta wannan

Matsiyata Kawai: Fasto Yayi wa Masu Bauta Tatas Bayan Sun Gaza Siya Masa Agogo Mai Tsada

"Gida ba kadara bace mai cigaba da cin kudi, kada ka ruda jama'a. Toh da kyau, a ce ka zuba kudin a kasuwanci, me zaka yi amfani da kudin ka cigaba? Mutane da yawa gidan dai zasu gina."

Collins Maka:

"Wani lokacin kudin hayan da kake biya kowacce shekara ya isa a gina gida."

Mandy:

"Wannan ya faru da ni tun 2019 na fara gina gida amma har yanzu ina yi. Ban saka rufi ba balle kammalawa ba."

Matsiyata Kawai: Fasto Yayi wa Masu Bauta Tatas Bayan Sun Gaza Siya Masa Agogo Mai Tsada

A wani labari na daban, wani fasto daga garin Missouri dake Amurka yayi suna bayan bidiyonsa ya bayyana inda yake caccakar masu bauta kan yadda suka gaza siya masa agogon Movado mai matukar tsada.

A wa'azinsa, Fasto Carlton Funderburke na cocin Well dake Birnin Kansas, an ji a bidiyo yana sukar mambobin cocin inda yake kiransu da fatararru.

Babu shakka bidiyon ya janyo martani kala-kala a yanar gizo inda wasu ke alakanta shi da zama faston bogi wanda ya fito tatsar kudaden masu zuwa coci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel