Ayyiriri: Yariman Jordan Mai Jiran Gado Zai Angwance Da Kyakkyawar Amaryarsa ‘Yar Saudiyya, Hotuna

Ayyiriri: Yariman Jordan Mai Jiran Gado Zai Angwance Da Kyakkyawar Amaryarsa ‘Yar Saudiyya, Hotuna

  • An yi baikon Yariman kasar Jordan mai jiran gado, Hussein bin Abdullah II da zukekiyar amaryarsa yar Saudiyya
  • A ranar Laraba, 17 ga watan Agusta ne yan uwa suka shaida baikon Yarima Hussein bin Abdullah II da Rajwa Khaled Al-Saif
  • An gudanar da taron wanda ya samu halartan sarki Abdullah II, sarauniya Rania da Yarimomin Jordan a gidan mahaifin Rajwa da ke Saudiyya

Saudiya - Yariman kasar Jordan mai jiran gado, Hussein bin Abdullah II zai angwance da budurwarsa ‘yar kasar Saudiya, Rajwa Khaled Al-Saif.

Jaridar Zawya ta rahoto cewa an yi baikonsu a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta, kamar yadda Kotun masarautar Hashemite ta Jordan ta sanar.

An yi bikin baikon ne a gaban mai martaba sarkin Jordan, Abdullah II, Sarauniya Rania da kuma yan uwan amaryar a garin Riyadh ta kasar Saudiya.

Kara karanta wannan

Mazauna a Kaduna sun fusata, sun sheke wata wata mai boye 'yan bindiga a gidanta

Yariman Jordan da amaryarsa
Ayyiriri: Yariman Jordan Mai Jiran Gado Zai Angwance Da Kyakkyawar Amaryarsa ‘Yar Saudiyya, Hotuna Hoto: Life in Saudi Arabia
Asali: Facebook

Hakazalika taron wanda ya gudana a gidan mahaifin amaryar ya samu halartan Yarima Hassan bin Talal, Yarima Hashem bin Abdullah II, Yarima Ali bin Hussein, Yarima Hashem bin Hussein, Yarima Ghazi bin Mohammed, Yarima Rashid bin Hassan, da kuma wasu ahlin Al-Saif.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarauniya Rania ta je shafinta na Twitter domin taya masoyan murna tare da nuna tsantsar farin cikin da take ciki.

Ta rubuta:

“Ban yi tsammanin zan iya rike wannan tarin farin ciki a zuciyata ba! Ina taya babban yarima Hussein da kyakkyawar amaryarsa Rajwa murna.”

Ga karin hotunan baikonsu a kasa:

Hotunan Kyakkyawar Budurwar Da Ta Lashe Gasar Karatun Al-Kur’ani A Arewacin Amurka, Ta Samu Kyaututtuka

A wani labarin, wata matashiyar budurwa mai suna Fartun wako ta lashe gasar karatun Al-Qur’ani na Imam Shatibi inda ta zo ta daya.

Sakamakon wannan bajinta da kyakkyawar budurwar ta yi an bata kyautar dankareriyar mota kirar 2022 Toyota Highlander sabuwa fil, kudi da kuma kujerar zuwa aikin Umrah.

Kara karanta wannan

Bidiyon Bikin Dan Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura Da Zukekiyar Amaryarsa Yar Kasar Waje, An Sanya Masa Lalle

Kamar yadda shafin Converts to Islam ya wallafa a Facebook, sama da dalibai 530 ne suka shiga gasar a wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng