Hotunan Yadda Matasa Suka Wanke Hanyar Da Atiku Ya Bi Bayan Ya Ziyarci Mahaifarsa Da Ruwa Da Sabulu

Hotunan Yadda Matasa Suka Wanke Hanyar Da Atiku Ya Bi Bayan Ya Ziyarci Mahaifarsa Da Ruwa Da Sabulu

  • Matasa sun gudanar da zanga-zanga a garin Jada, mahaifar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar
  • Kamar yadda ya bayyana a soshiyal midiya, matasan sun yi zanga-zanga ne a kan dawowarsa gida tare da ikirarin cewa bai tsinanawa mahaifarsa komai ba
  • An gudanar da zanga-zangar ne cikin lumana tare da wanke hanyar da ya bi ya shigo garin

Adamawa Wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga a mahaifar Atiku Abubakar da ke karamar hukumar Jada da ke jihar Adamawa, yan awanni bayan dawowar tsohon mataimakin shugaban kasar.

Abubakar Sadiq Kurbe ne ya wallafa hotunan zanga-zangar wanda aka yi cikin lumana a shafinsa na Twitter.

Matasa
Hotunan Yadda Matasa Suka Wanke Hanyar Da Atiku Ya Bi Bayan Ya Ziyarci Mahaifarsa Hoto: @SadeeqKurbe
Asali: Twitter

Kamar yadda ya bayyana a hotunan, an gano matasa suna amfani da ruwa da sabulu wajen wanke yankunan da dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar PDP ya bi yayin da ya ziyarci mahaifar tasa.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa IBB ya rigamu gidan gaskiya

Wallafar tasa ta zo kamar haka:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Matasan Adamawa suna wanke hanyar Jada bayan ziyarar Atiku. Atiku ya kasa gina hanya da yake matsayin mataimakin shugaban kasa amma yana bin hanyar da shugaban kasa @MBuhari ya gina wajen zuwa neman goyon bayanmu, ta yaya hakan zai faru.”

Yan Najeriya sun yi martani

@ikenga_power ya ce:

“LOL….Wannan karya ne kuma yakamata kamata ka ji kunyan kanka. Mutanen Adamawa na son Waziri ba tare da la’akari da siyasa ba.

@Sulaiman_msd ya ce:

“Lol karya.”

@NaijaFirst2023 ya ce:

Ta yaya wannan zai zama gaskiya, alhalin @Atiku ne ke da yawan ma’aikata da aka dauka aiki a jihar.”

@official_Hanif7 ya ce:

“Kyale wawan bama bukatarsa a matsayin shugaban kasa gara mu zabi Obi da mu zabe shi sai @officialABAT da @KashimSM 2023"

Mustapha Gajibo Ya Kera Motocin Bas Masu Amfani Da Lantarki, Hotunan Sun Kayatar Da Mutane

Kara karanta wannan

Yan Majalisu Biyu Da Dubbannin Yan Siyasa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Gangamin Atiku

A wani labarin, Yan Najeriya a soshiyal midiya sun cika da murnar ganin sabbin motocin bas masu amfani da lantarki wanda Injiniya Mustapha Gajibo ya kera a Maiduguri.

Gajibo wanda ya kasance sanannen injiniyan makamashi ya wallafa kayatattun hotunan sabbin motocin bas din a shafinsa na Twitter wanda ya burge mutane da dama.

An tattaro cewa sabbin motocin bas din mai cin mutum 12 zai iya gudun kilomita 212 bayan chaji daya tare da shafe tsawon kilomita 110 duk awa daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng