Yadda Wasu Mazauna a Kaduna Suka Kashe Wata Mata Saboda Kulla Harkalla Da ’Yan Bindiga
- Wasu fusatattun mazauna karamar hukumar Lere a jihar Kaduna sun kashe wata mata mai suna Hajiya Bilkisu, wacce aka gano tana ba 'yan bindiga mafaka
- An gano hakan ne bayan da dakarun Operation Safe Haven ta rundunar sojojin Najeriya suka cafke ‘yan bindigan a ranar Talata, 17 ga watan Agusta
- Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lere, jihar Kaduna - Wasu fusatattun matasa sun hallaka wata mata Mariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna, Hajiya Bilkisu, bayan da aka gano cewa tana boye barayin da ake nema ruwa a jallo a gidanta.
Mambobin al’ummar yankin sun samu labarin haka ne bayan da sojojin ‘Operation Safe Haven’ suka cafke ‘yan bindigar a gidan Bilikisu, kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar.
Aruwan ya bayyana sunayen ‘yan fashin da Bilikisu ke ba mafaka kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Musa Adamu
- Abdullahi Usman
- Suleiman Hasidu
- Usman Jibril
- Saidu Isah
- Hassan Abdulhamid
- Idris Sani
Kwamishinan ya bayyana cewa an kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri game da motsinsu.
Hakazalika, kwamishinan ya bayyana jin dadin gwamnatin Kaduna na kame 'yan ta'addan, tare da umartar su da ci gaba da yin cikakken bincike, haka nan 21 Century Chronicle ta ruwaito.
A bangare guda, ya gargadi mazauna da su daina dokar a hannu, su kasance masu hada kai da jami'an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a yankunansu.
Yadda Wani Dalibin Kwalejin da Ya Yi Barazanar Sace ‘Provost’ Dinsu, Ya Shiga Hannu
A wani labarin mai kama wannan, a jihar Neja, wani dalibi ya ba da mamaki yayin da ya tura wasikar baranza ga shugaban kwalejin da yake karatu da sunan yunkurin sace shi.
Jami'an Hukumar tsaron Najeriya ta NSCDC, ba su yi kasa a gwiwa ba, sun yi nasar kwamushe wannan matashi mai shekara 18.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin NSCDC, ASC Nasir Abdullahi, ya fitar, The Nation ta ruwaito.
Asali: Legit.ng