Majalisa Na Binciken Ministoci, An Bada Kwangilar Share Daji a Naira Biliyan 18.6
- Wani kwamiti a majalisar wakilan tarayya ya na binciken ma’aikatar gona da raya karkaran Najeriya
- Ma’aikatar ta bada kwangilolin N18bn domin gyaran kasa, ‘Yan majalisa ta na da shakku a kan ayyukan
- Za a kira kamfanonin da aka ba wadannan kwangiloli domin su yi wa majalisar tarayya karin bayani
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Kwamitin asusun gwamnati a majalisar wakilan tarayya sun shiga binciken Ma’aikatar harkar gona da raya karkaka na kasa kan zargin wata badakala.
Shugaban wannan kwamiti Oluwole Oke (PDP, Osun) ya bayyana wannan a ranar Talata, 16 ga watan Agusta 2022, Premium Times ta kawo wannan labarin.
Honarabul Oluwole Oke ya yi jawabi yayin da majalisa ta kira jama’a domin jin ta bakinsu game da kudin da aka kashe tsakanin 2013 da 2021 wajen share jeji.
‘Dan majalisar yake cewa an fitar da biliyoyi a wannan lokaci da sunan za a share daji ko gyaran kasa. Babu tabbacin cewa an yi wadannan ayyuka a Najeriya.
Jaridar tace Oluwole Oke yace wakilin ma’aikatar ya bayyana a gaban kwamitinsa, amma ‘yan majalisar tarayya ba su gamsu da bayanin da aka yi masu ba.
Akwai alamar tambaya
“Mun gayyaci ma’aikatar gona, kuma sun yi mana bayani. Amma wasu ‘yan kwamitinmu da a mazabunsu ake cewa an yi ayyukan, sun nuna shakkunsu.”
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Saboda ganin an yi adalci, mun gayyaci kamfanonin da aka ba kwangilolin, su zo suyi wa kwamitin nan bayanin wuri da lokacin da suka yi ayyukan.”
- Honarabul Oluwole Oke
A cewar Hon. Oke, kwamitinsu za iyi bakin kokarinsa na tursasawa kamfanonin hallara a gabansu.
Su wanene aka ba kwangilolin?
A rahoton da mu ka samu a ranar Laraba, ‘dan majalisar bai bayyana sunayen kamfanonin da aka gayyata ba, sannan ba mu da masaniyar ranar da za a kira su.
Mun fahimci cewa Intel Region ta kawo wani rahoto da ya saba kadan, tace an cire wadannan kudi ne a lokacin annobar COVID-19, yayin da kowa yake zaman gida.
Muhammad Mahmood shi ne Ministan harkar gona da raya karkara a Najeriya. Mahmood ya karbi aikin ne daga hannun Sabo Nanono wanda aka tsige a 2021.
Canzawa Kaduna suna
An yi shekara da shekaru ana kiran Kaduna da Jihar Kaduna a Najeriya, sai ga rahotanni na cewa ‘Yan Majalisar Dattawan kasar nan za su canza mata suna.
Rade-radin da ake yi shi ne za a koma kiran Kaduna da jihar Zazzau, amma an samu rahoto cewa Sanata Uba Sani ya karyata wannan, yace sam ba gaskiya ba ne.
Asali: Legit.ng