Tururuwa, Maciji, Biri Da Wasu Jerin Dabbobi Da Aka Taba Zarga Da Wawure Miliyoyin Nairori
A kwanan nan ne hukumar NSITF ta zargi tururuwa da cinye wasu takardu da ke kunshe da bayanai na kudade da ta kashe har naira biliyan 17.158
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
A baya an zargi wasu dabbobi irin su maciji, biri da sauransu da wawure miliyoyin kudade na gwamnati
Babban abun da ke damun mutane shine yadda maganar ke mutuwa murus ba tare da an kara jin batun ba
Abuja - Yan Najeriya na yawan wayar gari da labarai na zarge-zargen cin hanci rashawa masu ban mamaki wadanda suka kunshi makudan kudade na fitar hankali.
Sai dai kuma, a baya-bayan nan ana ta zargin dabbobi da wawure makudan kudade ko kuma ace sun cinye takardun kudade.
Wannan al’amari ya zama ruwan dare a yanzu domin yanzu haka ake shirya labari a duk lokacin da aka bankado wata badakala ta kudade.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, annan salo mai ban mamaki na zargin dabbobi da wawure kudade ba tare da an gano bakin zaren ba ya dade yana haifar da martani masu cike da rudani.
A wannan zauren, Legit.ng Hausa ta tattaro wasu jerin dabbobi da aka taba zarga da cinye kudade a Najeriya.
1. Tururuwa ta cinye takardun kudi N17.158bn da aka kashe a hukumar NSTIF
An zargi tururuwa da cinye wasu takardun da ke dauke da cikakkun bayanai na yadda aka kashe wasu kudade da yawansu ya kai N17.158bn a Asusun inshora na Najeriya, NSITF.
An tattaro cewa wadannan takardu na kunshe da bayanai kan yadda hukumar ta sarrafa kudin a 2013.
Mahukunta a hukumar sun bayyana hakan ne yayin da suka bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da asusun gwamnati.
Shugabar hukumar mai ci, Michael Akabogu, ya ce takardun na hannun hukumar.
2. Maciji ya hadiye N36m
A 2018, an dakatar da wata jami'ar hukumar JAMB, Philomena Chieshe, bayan ta bayyana cewa wani maciji ya hadiye kudi naira miliyan 36 da aka tara daga siyar da ‘katin JAMB.
Wata wakilai hukumar ta JAMB, Fabian Benjamin, ta bayyana cewa jami’ar ta bayyana cewa lallai maciji ne ya hadiye kudin da aka nema aka rasa.
Ta yarda cewa ta karbi kudaden sannan ta ajiye a wani durowan ofis, amma sai macijin ya je ya hadiye kudin.
3. Goggon biri ya hadiye N6.8m
A 2019, an zargi wani goggon biri da hadiye kudi naira miliyan 6.8 a gidan Zoo na Kano.
Wani mai kula da asusun gidan zoo din ya bayyana cewa wani goggon biri ne ya shige wani ofis sannan ya wawure kudaden kafin ya kuma hadiye su.
Shugaban gidan Zoo din, Umar Kabo ya tabbatar da batan kudaden kuma ya ce gwamnatin jihar na gudanar da bincike kan lamarin.
4. Biri ya hadiye N70m
A watan Fabrairun 2018, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa biri ne ya lakume kudi naira miliyan 70 da aka baiwa shugaban kungiyar sanatocin arewa a gonarsa.
Sani ya bayyana hakan ga manema labarai ne yan mintuna bayan an tunbuke Sanata Abdullahi Adamu daga matsayin shugaban kungiyar sanatocin arewa.
A wancan lokacin, an zargi sanata Adamu da yin almubazaranci da naira miliyan 70 mallakin kungiyar.
Sani yace kamar yadda sanatan da aka tunbuke ya bayyana, wasu birrai ne suka hadiye kudaden.
Mustapha Gajibo Ya Kera Motocin Bas Masu Amfani Da Lantarki, Hotunan Sun Kayatar Da Mutane
A wani labari na daban, Yan Najeriya a soshiyal midiya sun cika da murnar ganin sabbin motocin bas masu amfani da lantarki wanda Injiniya Mustapha Gajibo ya kera a Maiduguri.
Gajibo wanda ya kasance sanannen injiniyan makamashi ya wallafa kayatattun hotunan sabbin motocin bas din a shafinsa na Twitter wanda ya burge mutane da dama.
An tattaro cewa sabbin motocin bas din mai cin mutum 12 zai iya gudun kilomita 212 bayan chaji daya tare da shafe tsawon kilomita 110 duk awa daya.
Asali: Legit.ng