Hukumar EFCC ta shiga maganar batan miliyan N36m da maciji ya hadiye

Hukumar EFCC ta shiga maganar batan miliyan N36m da maciji ya hadiye

- An nemi kudi miliyan N36m a hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) an rasa

- Jami'in dake da alhakin ajiyar kudin ne ya ce 'wai' maciji ne ya hadiye su bayan an nemi kudin an rasa

- Yanzu haka dai hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci da rashawa, ta shiga maganar domin makure wannan maciji ya amayar da kudin da ya hadiya

A daya daga cikin labaran Legit.ng kun karanta wani labari mai kama da rainin hankali inda wani jami'in hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ya ce 'wai' maciji ne ya hadiye kudin hukumar da adadin su ya kai har Naira miliyan N36m.

Duk da batun batan kudin laifi ne mai alaka da cin hanci, 'yan Najeriya sun dauki abin da wasa ta hanyar yin raha da batun.

Hukumar EFCC ta shiga maganar batan miliyan N36m da maciji ya hadiye
Jami'an Hukumar EFCC

Har yanzu batun batan kudin na ci gaba da jawo cece-kuce a dandalin sada zumunta inda 'yan Najeriya ke bayyana mabanbantan ra'ayi a kan lamarin.

A yayin da wasu 'yan Najeriya ke shawartar hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da ta fara gurfanar da macizai masu hadiye kudin jama'a, hukumar JAMB ta mika lamarin ga hukumar ta EFCC domin binciken jami'in hukumar dake da alhakin ajiyar kudin domin gudanar da bincike a kansa.

DUBA WANNAN: Kasuwar bukata: Bayan rubuta wasika ga Buhari, ana kallon-kallo tsakanin magoya bayan Babangida da na Obasanjo

A wani sako da hukumar EFCC ta saki a shafinta na dandalin Facebook a yau, ta ce mikiyar hukumar za ta makure macijin da ya hadiye kudin hukumar JAMB har sai ya yi aman kudin da ya hadiye.

Hukumar ba tayi karin haske a kan binciken lamarin ba, sai dai ta ce zata sanar da jama'a nan bada dadewa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel