Bidiyon Yadda Wani Direba Ya Ci Na Kare Bayan Ayarin Gwamna Sun Tare Shi Kan Karya Dokar Tuki
- An sha wata yar dirama tsakanin wani direban mota da jami'an tsaro da ke cikin ayarin motocin gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu
- Direban yana tuki ne ba tare da bin doka ba don haka sai jami'an tsaron gwamnan suka tsare shi, yana ganin haka sai ya kwasa a guje ya bar motarsa a titi
- Mutanen da suka ga bidiyon a shafukan soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu, da dama sun ga laifin direban
Lagas - Wani direban mota ya haddasa yar karamar dirama a kan titin Lagas a ranar Talata, 16 ga watan Agusta.
Diraban dai ya yasar da motarsa a tsakiyan titi sannan ya ci na kare bayan jami’an tsaro da ke tare da ayarin motocin gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu sun tsayar da shi.
Kamar yadda shafin LIB ya rahoto, direban yana tuki ne ba tare da bin dokar tuki a hanya ba kwatsam sai ya ci karo da ayarin motocin gwamnan.
Saboda tsoron kada a kama shi, sai kawai ya ci na kare sannan ya yi watsi da motar tasa a kan hanya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu kan lamarin
latashalagos ta ce:
"Wai mai zai hana mu yin abu yadda yakamata kamar mutanen da ke son kasa mai inganci?
iam.gifted.g ya ce:
"Motarsa ta tafi ."
officialmurphy1 ya ce:
" yanzu a zuciyarsa zai dunga cewa azzalumansa sun zo amma kuma ba zai bi doka da zama dan kasa nagari ba."
jersey.collections ta ce:
" yan haka ina kasa ina birgima da dariya ."
nkiruka734 ta ce:
"Me yasa kake gudu."
ifedirich ya ce:
"har yana umurtansu da su rufe masa kofa."
Ana Shagali A Lagas: Bidiyon Dan Achaba Yana Jan Motar Bas Mai Cin Mutum 18 Da Igiya
A wani labarin, jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyana bidiyon wani dan achaba yana jan motar bas mai cin mutane 18.
A cikin bidiyon wanda tuni ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano yadda aka daure motar bas din wacce ga dukkan alamu ta samu matsala ne a jikin babur din da igiya.
Sai direban babur din ya dungi jan motar a kan titi wanda ke dauke da cunkoson ababen hawa.
Asali: Legit.ng