Allah Ya Yiwa Tsohon Kakakin Shugaban Kasa IBB, Duro Onabule Ya Rasu
- Labarin da ke iso mu ya bayyana cewa, Allah ya yiwa tsohon mai magana da yawun shugaban kasa IBB rasuwa
- Mambobin kungiyar tsoffin dalibai na makarantar da ya yi karatu sun nuna jimami da rashin wannan babban jigo
- CPS Duro Onabule ya kasance mai magana da yawun IBB har zuwa karshen mulkin soja a wancan zamanin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Legas - Allah ya yi wa tsohon babban sakataren yada labarai na tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida, CPS Duro Onabule rasuwa.
Shahararren dan jaridan ya rasu yana da shekaru 83 kuma an ce ya rasu ne a ranar Talata 16 ga watan Agusta.
Babu cikakken bayani game da mutuwarsa har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Amma an sanar da lamarin a dandalin Old Grammarians’ Society (OGS) na Makarantar Grammar ta CMS da ke Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onabule ya yi karatu a makarantar ta CMS kuma ya kasance tsohon dalibi mai sadaukarwa ga kungiyar daliban, kamar yadda mambobin kungiyar suka bayyana.
Marigayin ya kasance editan Jaridar National Concord tsakanin 1984 zuwa 1985 kafin a nada shi a matsayin Babban Sakataren Yada Labarai na Shugaba Babangida.
Onabule ya kasance mai magana da yawun shugaban kasa a kusan duk zamanin mulkin soja, haka nan The Guardian ta ruwaito.
Mun girgiza, inji abokan karatunsa
Da yake mayar da martani game da rasuwarsa, Sakataren Yada Labarai na OGS na kasa, Otunba ‘Dare Odufowokan, ya bayyana marigayi Onabule a matsayin tsohon dalibi wanda ya cancanci yabo, mai kishin al’umma da na kasa dashi.
A cewar shugaban na OGS:
“Ya kasance daya daga cikin manyan daliban makarantar Grammar da muke ji dashi. Yana da kyakkyawan suna a harkar yada labarai wanda ya zaburar da yawancin 'yan makarantar Grammaer tsawon shekaru kuma yana alfahari da kasancewarsa memban kungiyar.”
Ku Nemi Taimakon Ubangiji Kan Al'amuran Siyasarmu, IBB Ga 'Yan Najeriya
A wani labarin, Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, yace 'yan Najeriya su nemi taimakon Ubangiji kan alkiblar da zasu dosa a al'amuran siyasar kasar nan.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Babangida ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Niger domin tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa.
Tsohon shugaban kasan ya cika shekaru 81 a ranar 17 ga watan Augustan 2022. A jawabinsa, yayi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da yin imani wurin hadin kan kasar nan tare da mayar da hankali da sa ran cewa komai zai daidaita.
Asali: Legit.ng