Har Yanzun Fasinjojin Jirgin Ƙasan Kaduna Na Hannun Yan Ta'adda, Suna Tsaka Mai Wuya, Mamu

Har Yanzun Fasinjojin Jirgin Ƙasan Kaduna Na Hannun Yan Ta'adda, Suna Tsaka Mai Wuya, Mamu

  • Tukur Mamu, wanda a baya ya kasance mai shiga tsakani, ya tabbatar da cewa labarin sako ragowar fasinjojin jirgin kasan Kaduna ƙarya ne
  • Ɗan jaridan, makusancin Sheikh Ahmad Gumi, ya ce akwai sauran Fasinjoji 27 a cikin jeji kuma suna hali mai matuƙar muni
  • Kusan watanni buyar kenan da kai harin, yan ta'adda sun sako wasu fasinjojin rukuni-runkuni, har yanzun wasu na tsare

Kaduna - Fitaccen ɗan jaridar nan, Tukur Mamu, ya musanta rahoton da wasu kafafen watsa labarai da shafukam sada zumunta ke yaɗawa cewa yan ta'adda sun sako sauran Fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna.

Aminiya ta tattaro cewa Mamu, wanda ke shiga tsakani don tattauna wa tsakankn FG da yan ta'addan, ya ce zuwa yau akwai sauran Fasinjoji 27 a hannun su, kuma suna cikin yanayi mai muni.

Kara karanta wannan

Duk wanda aka gani a harbe: Gwamnatin Zamfara ta haramta hawa babura a wasu yankuna

Tukur Mamu
Har Yanzun Fasinjojin Jirgin Ƙasan Kaduna Na Hannun Yan Ta'adda, Suna Tsaka Mai Wuya, Mamu Hoto: Withinnigeria.com
Asali: UGC

Tukur Mamu, makusancin fitaccen malamain addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya tabbatar da haka ne a wata sanarwada ya fitar ranar Talata, 16 ga watan Agusta, 2022.

Bayan sako mutanen rukuni-rukuni, Mamu ya bayyana cewa akwai ragowar Fasinjoji 27 a sansanin yan ta'addan waɗan da zuwa yanzu suka shafe kusan kwanaki 150 a hannun su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, tuni ya tsame jikinsa daga tattauna wa da yan ta'addan, kuma ya zare hannunsa baki ɗaya kan lamarin, duk da a baya shi ne ya shiga tsakani har wasu suka kubuta.

Bugu da kari ya ce ya fitar da wannan sanarwan ne bayan yan uwan fasinjojin da yan jarida da ke son sanin gaskiya sun matsa masa lamba don tabbatar da sahihancin labarin.

Premium Times ta rahoto Mamu ya ce:

"Ina tabbatar wa ba tare shilafa ba cewa har yanzun fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja 27 na hannun yan ta'adda, kusan watanni biyar kenan bayan faruwar lamarin."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Da Yawa Sun Mutu Yayin Da Suka Yi Yunkurin Kai Mummunan Hari Garuruwa Biyu a Jihar Katsina

"Duk da na tsame hannu na a lamarin, iyalai, yan jarida da wasu yan Najeriya da suka damu sun matsa mun da kira suna son jin sahihancin labarin yayin da tuni wasu suka fara murna suna taya juna murna."
"Kasancewar kowa ya ƙagu ya ji labarin hakan ya ba wasu gurɓatattun masu son yaɗa labari mara tushe, ƙarya, kuma labarin zai ta da hankalin dangin ragowar fasinjojin da miliyoyin yan Najeriya da ke fatan Alheri."

Wane hali suke ciki?

Mamu ya ƙara da cewa har yanzun ragowar fasinjojin na tsaka mai wuya, wasun su ba su da lafiya sannan kuma yanayin ruwan damina na shafar su fiye da tunani.

"Ina rokon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nunka kokarinsa wajen ceto ragowar da ke hannun yan ta'adda domin halin da suke ciki ya fi gaban kwatance."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Da Yawa Sun Mutu Yayin Da Suka Yi Yunkurin Kai Mummunan Hari Garuruwa Biyu a Jihar Katsina

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Jiragen NAF Sun Yi Ruwan Wuta Kan Tulin Yan Ta'adda a Jihohin Arewa Biyu

Yan ta'adda ya yawa sun sheƙa barzahu yayin da suka yi yunkurin kai hari kauyuka biyu a jihar Katsina.

Hukumar yan sanda ta ce ta samu labarin zuwan yan ta'adda, nan take ta tura dakaru yankin ƙaramar hukumar Kurfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262