Yanzu-yanzu : Sojoji Sun Sake Kashe Yanta’adda Da Dama A Jihar Kaduna
- Dakarun sojojin Operation Sanity sun kara kashe wasu yan bindiga a dajin gulbe dake karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna
- Yanta'adan da sojoji suka kashe sun gamu da karshen sun ne a lokacin da suka je kwashe gawarwakin yan uwansu da aka kashe a ranar Asabar
- Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sjoji za su cigaba da kai hari a duk inda yanta'adda suka a fadin jihar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Kaduna - Dakarun sojojin Operation Sanity sun kara kashe wasu yan bidiga a wata arrangama da sukayi a dajin gulbe dake karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna. Rahoton Leadership
Hakan na zuwa ne bayan kwanaki uku da sojoji suka kashe wasu yan bidiga da yawa.
A water sanarwa da kamfanin tsaro ma zaman kanta na Eons Intelligence, ta fitar a shafin na Tuwita a ranar Talata, ta ce yan ta’adan sun gamu da karshen su ne yayin da suka zo kwashe gawarwakin yan uwan su da sojojin suka kashe ranar Asabar.
Legit.NG ta rawaito labarin rahoton da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar a ranar Asabar akan nasarar da dakarun sojoji sama da na kasa suka samu wajen kashe yan bindiga da dayawa a sabuwar atisayen dake suke gudanarwa a dazukan jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwamishinan ma’aikatar tsaron na cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya fitar da sanarwar a ranar Asabar, inda ya ce an kashe ‘yan ta’addan ne a Galbi da ke karamar hukumar Chikun ta jihar.
Aruwan ya cigaba da cewa dakarun sojoji za su cigaba da gudanar da atisaye u duk wuraren da aka gano maboyan yan ta’adda ne a fadin jihar kaduna.
IGP Ya Karrama DPO A Jihar Kano Saboda Yaki Karbar Cin Hancin Makudan Daloli Da Aka Bashi
A wani labari kuma Abuja - Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ya karrama DPO na Unguwar Nasarawa dake jihar Kano SP Daniel Itse Amah, da Satifiket din lambar yabo. Rahoton THE NATION
DPO na Unguwar Nasarawa SP Daniel, ya nuna bajinta da kwarewa a aikin sa, yayin da ya ki karba cin hancin dala USD 200,000 da aka bashi akan kamun wasu yan fashi da makami.
Asali: Legit.ng