Kaunar da Nake wa 'Yan Najeriya Bata Misaltuwa, Shugaba Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kaunar da yake wa 'yan Najeriya ba zata iya misaltuwa ba
- Ya sanar da cewa, duk da barazanar matsin rayuwa da tattalin arziki, ya shirya inganta rayuwar 'yan Najeriya
- Buhari ya sanar da hakan ne yayin da ya karba bakuncin tsohon shugaban tsohuwar jam'iyyar CPC a gidan gwamnati dake Abuja
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada burin mulkinsa na Inganta rayuwar 'yan kasa duk da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.
Ya ce burinsa na inganta rayukan 'yan Najeriya bai dishe ba, inda yake kira da 'yan Najeriya da su kara hakuri, jaridar Daily Nigerian ta rahoto.
Shugaban kasan ya bayar da tabbacin hakan ne lokacin da ya karba bakuncin tsohon shugaban tsohuwar jam'iyyar CPC a gidan gwamnati a Abuja, ranar Talata.
Ya kara da kira ga shugabannin siyasa da su mayar da hankali wurin tabbatar da sun daga darajar kasar nan.
Shugaban kasan yace son kan da ya janyo rashin miliyoyin rayuka tsakanin 1967 zuwa 1970 bai kamata a bari ya maimaita kansa ba.
Shugaban kasan wanda shi ne ministan man fetur, ya kara da amincewa da siyan kamfanin Mobil wanda Seplat Energy Offshore Ltd suka yi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
ExxonMobil, asalin kamfanin ya shiga yarjejeniyar siya da siyarwa da Seplat Energy wurin siyan dukkan hannayen jarin Mobil Production Nigeria Limited daga Exxon Corporation na USA.
Yarjejeniyar zata bai wa Seplat Energy damar siyan jari daga Mobil Development Nigeria da kuma Mobil Exploration Nigeria, dukkansu masu rijista a Delaware, USA.
Femi Adesina, kakakin shugaban kasan, ya sanar a ranar Litinin a Abuja cewa, wannan amincewar na tafe ne da burin Najeriya na samun karin shiga a fannin makamashi.
Hakazalika a ranar Litinin, shugaban kasan ya taya ma'aikatar matasa da wasanni murna kan kokari da kwazon da suka gwada a wasannin Commonwealth a Birmingham, UK.
2023: Peter Obi Ya Caccaki APC da PDP Kan Gaza Gyara Wutar Lantarki Tsawon Shekaru 24
A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi ya caccaki jam’iyyar APC mai mulki da PDP kan gazawar da suka yi a bangaren mulki tsawon shekaru.
Kamar yadda jaridar Daily Independent ta ruwaito, Obi ya yi tsokaci kan gazawar jam’iyyun siyasar biyu ne wajen gyara wutar lantarki bayan shafe shekaru 24 a kan karagar mulki.
Asali: Legit.ng