Bayan Gwamna Ya sha Kaye, An Sanya Ranar Zaɓen Kananan Hukumomi a Osun

Bayan Gwamna Ya sha Kaye, An Sanya Ranar Zaɓen Kananan Hukumomi a Osun

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Osun ta zaɓi ranar 15 ga watan Oktoba, 2022 a matsayin ranar zaɓen kananan hukumomi
  • Shugaban hukumar, Segun Oladitan, ya ce suna cigaba da shirye-shirye ba dare ba rana bayan kawar da duk wasu matsaloli
  • A watan Yuli da ya gabata ne, hukumar INEC ta gudanar da zaben gwamnan Osun, wanda ɗan takarar PDP ya lallasa gwamnan APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Osun - Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun, OSIEC, ta tsayar da ranar da zata gudanar da zaɓen kananan hukumomi a jihar.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa hukumar ta sanya ranar 15 ga watan Oktoba, 2022 a matsayin ranar zaben shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli.

Taswirar jihar Osun.
Bayan Gwamna Ya sha Kaye, An Sanya Ranar Zaɓen Kananan Hukumomi a Osun Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban OSIEC, Mista Segun Oladitan, shi ne ya bayyana haka ranar Litinin 15 ga watan Agusta, 2022, sa'ilin da yake zantawa da manema labarai a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Kara karanta wannan

El-Rufai da Shugabannin Arewa Ta Yamma Sun Gabatar Wa Tinubu Jerin Manyan Muƙaman da Suke Bukata

Shugaban hukumar ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba da jimawa ba majalisar dokokin jihar Osun ta zartar da dokokin hukumar zaɓen jiha mai zaman kanta 2022 kuma gwamna ya rattaɓa hannu a kai.
"Zuwa yau, duk wasu kalubale da yanayi sun zama tarihi, bisa haka hukumar zabe ta samu damar gudanar da zaɓen kananan hukumomi. Duk wasu dokokin game da zaɓen kananan hukumomi a baya an warware su."
"Hukumar na farin cikin shaida maka da baki ɗaya al'umma cewa zata gudanar da zaɓen kananan hukumomin jihar Osun, Najeriya ranar 15 ga watan Oktoba, 2022."

Wane irin shiri hukumar ke yi?

Daily Trust ta ce da yake jawabi kan dabaru da tsarin da hukumar ta shirya gudanar da zaɓen wannan karon, shugaban ya ce:

"Ina mai farin cikin sanar da ku cewa wannan lokacin zamu gudanar da zaɓen ne ta hanyar tsarin shugaba, inda za'a zaɓi Ciyamomi kai tsaye kana a zaɓi Kansiloli daban."

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo Ya Gargaɗi Yan Najeriya Kan Abu Ɗaya da Zai Iya Rusa Najeriya a 2023

Bugu da ƙari ya ce hukumar ba ta zauna ba, tana cigaba da tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma shirye-shirye ɗaya bayan ɗaya domin gudanar da zaɓen.

A wani labarin kuma Gwamna gwamna Ganduje ya aike da sunayen sabbin Kwamishinoni 8 majalisar dokoki

Gwamnan jihar Kano ya naɗa sabbin kwamishinoni Takwas, ya tura da sunayen su ga majalisar dokoki domin tantance wa.

A zaman majalisar na yau Litinin, Kakaki ya karanta sunayen mutanen, waɗan da zasu maye gurbin tsoffin da suka yi murabus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262