Gwamna Ganduje Ya Aike Da Sunayen Sabbin Kwamishinoni 8 Majalisar Dokoki
- Gwamnan jihar Kano ya naɗa sabbin kwamishinoni Takwas, ya tura da sunayen su ga majalisar dokoki domin tantance wa
- A zaman majalisar na yau Litinin, Kakaki ya karanta sunayen mutanen, waɗan da zasu maye gurbin tsoffin da suka yi murabus
- Majalisa ta kuma zaɓi ranar 22 ga watan Agusta a matsayin ranar da zata fara aikin tantance kwamishinonin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Gwamnan jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, Dakta Abdullahi Ganduje, ya aike da sunayen sabbin kwamishinoni Takwas ga majalisar dokokin jihar.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da babban mai taimaka wa kakakin majalisar dokokin, Isa Ɗan Abba, ya fitar a shafin Facebook.
Sanarwan ta ce gwamna ya aike da sunayen mutum Takwas ɗin ne domin a tantance su kafin naɗa su kujerun kwamishinoni a gwamnatinsa.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a zaman yau Litinin, kakakin majalisar, Injiniya Hamisu Chidari, ya karanta sunayen da ke ƙunshe a takaradar da gwamnan ya aike musu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwan ta ce:
"Mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya turo da sunayen mutum Takwas da ya zaɓa domin tantance su da tabbatar da su a matsayin sabbin kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwa a Kano."
Sunayen mutum 8 da Ganduje ya zaɓo
Ɗan Abba ya bayyana sunayen mutanen da gwamnan ya zaɓa don naɗa su kwamishinonin kuma ya tura ga majalisa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.
Mutanen sun haɗa da, Alhaji Ibrahim Ɗan'azumi Gwarzo, Abdulhamid Abdullahi Liman, Hon. lamin Sani Zawiyya da Rt. Hon. Ya'u Abdullahi 'Yan Shana.
Sauran kuma su ne; Honorabul Garba Yusuf Abubakar, Dakta Yusuf Jibrin Rurum, Hon. Adamu Abdul Panda, da kuma Alhaji Sale Kwasaimi.
Sabbin kwamishinonkn zasu maye gurbin da tsoffin suka bari, waɗan suka yi murabus domin tsaya wa takarar kujeru daban-daban a jihar.
Majalisar ta kuma gayyaci mutane Takwas da gwamnan aike mata domin tantance su ranar Litinin 22 ga watan Agusta, 2022.
A wani labarin kuma Yadda Gwamna El-Rufai da Jiga-Jigan APC a Arewa Ta Yamma Suka Bukaci Muƙamai a Gwamnatin Tinubu
Shugabannin APC reshen arewa maso yammacin ƙasar nan sun rubuta tare da gabatarwa Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa, jerin mukaman da suke buƙata idan an kafa gwamnati a 2023.
Wasu bayanai da suka fito sun nuna cewa gabanin Bola Tinubu, ya bayyana abokin takararsa, gwamnan Kaduna, Malam El-Rufai, ya jagoranci tawagar wakilan arewa ta yamma zuwa wurinsa.
Asali: Legit.ng