Goyon Kaka: Bidiyon Yar Karamar Yarinya Tana Kwaikwayon Kakanta, Harda Nade Hannu A Baya

Goyon Kaka: Bidiyon Yar Karamar Yarinya Tana Kwaikwayon Kakanta, Harda Nade Hannu A Baya

  • Wani bidiyo ya nuno wata yadda wata yar karamar yarinya ta dungi kwaikwayon tafiyar kakanta yayin da suke jerawa
  • A cikin bidiyon, an gano yarinyar tana tafiya sak irin na mutumin yayin da nade hannayenta a baya
  • Mutane da dama a shafukan soshiyal midiya sun yi martani ga abun da yarinyar tayi cewa dole mutum ya san abun da zai dunga yi a idon yara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gaskiya ne maganar cewa yara na kallon manya wajen fahimtar abubuwan da ke kewaye da su a duniya. Hakan ne yasa suke bi duk wani sahu nasu.

A wani bidiyo da ya yadu a shafin TikTok, an gano wata karamar yarinya tana jerawa kakanta inda ta dunga kwaikwayon duk wani motsi nasa.

Jika da kaka
Goyon Kaka: Bidiyon Yar Karamar Yarinya Tana Kwaikwayon Kakanta, Harda Nade Hannu A Baya Hoto: TikTok/@malikateeheart
Asali: UGC

Harma ta sanya hannayenta a bayanta sannan ta dunga tafiya kamar yadda tsohon ke tafiya. Abun ya baiwa mutane dariya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

Lokacin da mutumin ya mike daya daga cikin kafafuwansa a yayin da suke tafiyar, sai itama yarinyar tayi kamar yadda yayi. An yi rubutu a bidiyon kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Idan kana shafe tsawon lokaci da kakan ka.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

HONEY GOLD ta ce:

"Wannan ne dalilin da yasa yana da kyau a kodayaushe mutum ya dunga aikata alkhairi a gaban yara."

crispymunchies0 ta ce:

"Yara na kwaikwayon komai. Abun ya kayatar."

Donna Draper ta ce:

"aww diyar kaka ce."

Daga Wasa: Allkali Ya Aike Da Mai Wasan Barkwanci Gidan Maza Kan Firgita Banki Da Wasan Fashi Da Makami

A wani labarin, wani matashi dan shekaru 19 mai wasan barkwanci a Lagas, Eyinatayo Iluyomade, ya tsinci kansa a kurkuku bayan ya yi wasan barkwanci mai tsada ta hanyar ajiye wasikar fashi da makami a wani bankin zamani da ke garin Ondo, jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Bilkisu Mai Gadon Zinari: Bidiyon Yadda Aka Ciccibo Wata Amarya A Kan Wani Kasaitaccen Gado Kamar Na Sarauta

Yan sanda sun gurfanar da Iluyomade a gaban kotu kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, barazana da kuma tin abubuwan da za su iya kawo barazana ga tsaro, jaridar Vanguard ta rahoto.

Dan sanda mai kara, Akao Moremi, ya fada ma kotu cewa wanda ake kara ya ajiye wata takarda a bankin yana nuna cewa da misalin karfe 1:00pm na wannan rana, mambobin kungiyarsa na fashi da makami za su zo yin fashi a bankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng