Hotuna: Sarkin da Yafi Kowanne Basaraken Najeriya Karancin Shekaru ya Gama Sakandare, Yayi Jawabi

Hotuna: Sarkin da Yafi Kowanne Basaraken Najeriya Karancin Shekaru ya Gama Sakandare, Yayi Jawabi

  • Mai Martaba Oba Oloyede Adeyeoba Akinghare II, basaraken da yafi kowanne karancin shekaru a Najeriya, ya yi murnar kammala makarantar sakandare
  • Basakaren Ondon wanda da kadan ya wuce shekaru 17, ya je soshiyal midiya inda yayi godiya ga 'yan uwansa da mabiya kan goyon bayan da suka bashi har yayi shekaru 6 a makarantar kwana
  • Oba Oloyede yayi kira ga karin goyon baya daga jama'arsa yayin da yake hangen daukar nauyin dake kansa a lokacin da ya fara zama babban mutum

Ondo - Ma'abota amfani da soshiyal midiya sun taya Mai Martaba, Oba Oloyede Adeyeoba Akinghare II, Arujale na masarautar Okeluse, murnar kammala karatunsa na sakandare.

Basaraken jihar Ondon, wanda shi ne basarake mafi karancin shekaru a Najeriya, ya wallafa hotunansa na shagalin bikin gama makarantar sakandare a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Makarantar Sakandire a Jihar Arewa, Sun Aikata Mummunar ɓarna

Oba Adeyeoba
Hotuna: Sarkin da Yafi Kowanne Basaraken Najeriya Karancin Shekaru ya Gama Sakandare, Yayi Jawabi. Hoto daga @officialerujale_of_Okeluse
Asali: Instagram

Matashin basaraken ya mika godiyarsa ga dukkan 'yan uwansa da masarautarsa kan goyon bayan da suka bashi na tsawon shekaru shida har ya tafi makarantar kwana.

"Ina taya kaina murna na wannan shekaru shidan da na kwashe a makarantar sakandare yayin da ya zo karshe a yau. Na godewa Ubangiji madaukaki, iyayena, hakimaina, abokaina, masoyana da dukkan jama'ar masarautar Okeluse kan goyon bayan da suka bani na tsawon shekaru shida da nayi a makarantar kwana."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yayin da yake mika godiya da yabawa ga hukumar makarantar sakandare da malamansa, yayi kira kan karin goyon baya bisa nauyin dake kansa yayin da yake shiga kwaryar manya.

"Tafiya zuwa girma ta fara ne yanzu tare da nauyin dake kaina. Ina kira ga dukkan masoyana da su bani goyon baya saboda ba zan iya ni kadai ba, zan cigaba da dagewa wurin ganin cigaban masarautata, mutane na da kuma daga darajar kujerar kakanina," ya rubuta.

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro

Jama'a sun yi martani

@officialmykel_femo:

"Ina taya ka murna Alayeluwa."

@oladushmain4:

"Ina taya ka murna ranka shi dade. Karin nasara nake maka fata."

@theprincessayo:

"Ina taya ka murna sarkina."

Hotuna: Ɗan Sanata Ahmad Sani Yarima ya angwace da budurwarsa ƴar ƙasar Somalia a London

A wani labari na daban, labari da duminsa da Legit.ng ke tattaro muku shine na auren 'dan Sanata Ahmad Sani, Yariman Bakura da za a yi a birnin London.

Kamar yadda @fashionseriesng suka fitar a shafinsu na Instagram, an daura auren a ranar Juma'a, 5 ga watan Augustan 2022 a birnin London.

Asali: Legit.ng

Online view pixel