Yanzu dai kam mun gama da Boko Haram baki dayanta - Sojojin Najeriya bayan sun kame Sambisa
- An dade ana cewa an gama da Boko Haram, amma sai a ga sun dawo
- An gagara kama ko kashe Shekau, sai dai kurari
- A kasar Hausa ta'addanci ya sami zama a Sambisa
A jiya ne sojojin Najeriya suka saki hotunan kammala yaki da Boko Haramum a Sambisa, inda suka ce abin ya zo karshe.
An shafe shekaru 9 kenan ana yakar ta'addanci wanda kungiyar Ahlussunna ta da'awa, da jihadi ta faro a biranen Arewa, karkashin Malam Muhammadu Yusuf, da kuma Abubakar Shekau, a masallatai a Maiduguri.
Sabon salon Boko Haram dai bayan an ci galabar su, shine kashe kauyawa da yi musu fashi da sunan ghanima ta jihadi, da ma daura wa 'yan mata bam su fashe cikin jama'a. Su kan kuma sayar da mutane a maatsayin bayi kamar yadda ake yi a wadancan lookuuta na jihadi.
DUBA WANNAN: Daga kama barawo sai a kone shi?
A yanzu dai, Kwamanda na Operation Lafiya dole yace an kawo karshen Boko Haram a dajin na Sambisa, bayan sojojin su kakkabe karshen ta'addanci inji Manjo Nikolas Rogers, inda a harin Deep Punch, yace sun kwace sansani na daya na kungiyar, inda suka cika buhunhuna da littattafai na addini da ake karantar da Boko Haram din da su.
Ya kum kara da cewa, sun kame daruruwan mayakan, sun kuma kar da dama, sannan wasunsu kuma sun tsere sun bazama cikin daji. Sai dai sojin sun kasa gane cewa, watsewar 'yan ta'adda kan basu dama ne su dawo su hadu su ci gaba da iya shege.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng