'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa
- Shugaban TESCON ya shiga matsala kan tsokacin da aka kwatanta shi da na rashin ladabi da yayi kan ministan yankin arewa, Alhaji Saani Alhassan
- Sayibu Afa Yaba, shi ne Shugaban TESCON a jami'ar fasaha ta Tamale, ya wallafa cewa kamar ministan bai yi wanka ba kafin ganawa da Shugaban kasa
- An zargi cewa, 'yan sanda sun je har makaranta sun yi ram da shi a ranar Laraba, 10 ga watan Augustan 2022 zuwa wani wuri da ba a sani ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ghana - Shugaban kungiyar dalibai na jami'ar fasaha ta Tamale dake Ghana, Sayibu Afa Yaba, ya shiga hannun jami'an ,yan sanda.
Rahotanni sun bayyana cewa, an kama shi a ranar 10 ga watan Augustan 2022 kan wani tsokaci da yayi a soshiyal midiya da ake gani tamkar cin mutuncin ministan yankin arewaci, Alhaji Saani Alhassan.
Sayibu ya wallafa a Facebook cewa, alamu na nuna cewa Alhaji Alhassan bai yi wanka ba lokacin da ya jagoranci tawagar yi wa shugaba Akufo-Addo maraba a babban birnin yayin da yaje rangadi.
Kamar yadda rahotanni suka nuna daga Ghanaweb, kungiyar dalibai din ta sha mamaki kan wannan kamen.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Muna cikin makaranta yayin da wani jami'in 'dan sanda ya jagoranci tawaga suka kama abokin karatunmu. Daga yanda ya gabatar da kansa, zatonmu wasa ne. Kawai sai muka ga ya buga masa ankwa a hannu tare da aike shi caji ofis," shugaban SRC, Dauda Gafaru ya sanarwa gidan rediyon Tamale.
Ya kara da cewa: "Har tambayarmu aka yi idan ya dace yadda abokin karatunmu yayi wa ministan a Facebook," yace hakan ya tabbatar da cewa kamen an yi shi ne saboda wallafarsa ta Facebook.
Bidiyo: 'Dan Sandan Najeriya Ya Fitittike, Ya Ki Karbar Kudin da Direba Ya Bashi Kyauta
A wani labari na daban, wani jami'in 'dan sanda ya bayyana wadatar zucinsa a kan titi da irin albashin da yake samu ya ishe shi, lamarin da ya matukar birge jama'a.
Lamarin ya faru ne inda 'dan sandan ya ki karbar kudin da mutumin dake cikin mota ya bashi. 'Dan sandan ya jaddada cewa bai zai karba kyautar ba.
Bayan mutumin ya ga ya dinga mika kyautar kudinsa kuma an ki karba, ya fito da wayarsa inda ya nadi bidiyon jami'in 'dan sandan.
Asali: Legit.ng