Barayi Sun Kutsa Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Sun Sace Miliyoyin Kuɗi
- Ana zargin wasu ɓarayi sun shiga har cikin gidan gwamnatin jihar Katsina, sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe
- Wannan ba shi ke karo na farko a irin haka ta faru a gidan gwamnatin Katsina ba, ginin da ya kamata ya kasace mafi tsaro a jihar
- Tuni dai gwamnatin ta sanar da hukumar yan sanda kuma ta fara bincike don gano gaskiyar abinda ya faru
Katsina - Rahotannin da ke shigowa sun nuna cewa ana zargin wasu 'Ɓarayi' sun kutsa gidan gwamnatin jihar Katsina sun yi awon gaba da Miliyan N31m.
Wannan shi ne karo na biyu da aka yi irin wannan aika-aika ta sata a gidan gwamnati, wanda ya kamata ya kasance gini mafi tsaro a faɗin jihar.
A shekarar 2020, An sace makudan kuɗi da suka kai miliyan N16m a ofishin Sakatarem gwamnatin Katsina (SSG).
Premium Times ta ruwaito cewa a lokacin an kama jami'ai biyu da ke aiki a ofishin Sakataren da wani mai gadi ɗaya da zargin hannu a satar kuɗin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabuwar satar da aka yi
Wata majiya daga gidan gwamnatin ta shaida wa jaridar cewa lamarin satar kuɗin ta faru ne tun a ranar 31 ga watan Yuli, 2022.
Majiyar da ta nemi a sakaya bayananta ta ce wasu mutane da ba'a san ko suwaye ba sun kutsa ofishin mai kula da kuɗi na gidan gwamnatin, suka yi gaba da wasu kuɗi a buhu.
A cewarsa, satar ta auku ne da daddare lokacin mai kula da kuɗin, Salisu Batsari, yana cikin ofishin.
"Banga Kamarar CCTV ba amma kunsan tana daya daga cikin abubuwan da yan sanda zasu buƙata. Naji ance Kamarar ta ɗauki wani mutumi ya rufe fuskarsa lokacin da ya kutsa Ofis ɗin ta Taga."
Hadimin gwamnan Katsina, Al'Amin Isa, ya tabbatar da sace kudin ga manema labarai amma bai ce komai ba game da adadin kuɗin da aka rasa ba.
Mista Isa ya ƙara da cewa gwamnatin da hukumar yan sanda na kan bincike game da satar kuma babu tantama duk wanda ya aikata zai ɗanɗana kuɗarsa.
Shin an kama wasu da ake zargi?
Duk da kakakin hukumar yan sandan jihar, Gambo Isa, bai ce komai game da lamarin ba, amma wani ma'aikacin gidan gwamnatin ya ce an kama wasu jami'ai amma an sake su.
"Ranar Litinin da gwamnati ta fahinci an ɗauke kuɗin, cikin gaggawa ta shigo da yan sanda suka fara bincike. Mai kula da kuɗin da wasu ma'aikata da Masu gadi dake aiki a ranar yan sanda sun gayyace su don amsa tambayoyi."
Vangauard ta ce da aka tambaye shi dagaske yan sanda sun saki waɗan da ake zargin, ya ce ba shi da masaniya kasancewar ba ya cikin masu bincike.
A wani labarin kuma Tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya gargaɗi yan Najeriya kan abu ɗaya da zai rusa Najeriya a 2023
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya gargaɗi yan Najeriya su yi karatun ta nutsu wajen zaɓen 2023 da ke tafe.
Obasanjo ya ce idan aka yi kuskuren zaɓen shugabanni a zaɓe na gaba, Najeriya ka iya rushe wa.
Asali: Legit.ng