Obasanjo: A Duba Kwakwalwar Duk Wanda Ya Ce Abubuwa Na Tafiya Dai-Dai A Najeriya

Obasanjo: A Duba Kwakwalwar Duk Wanda Ya Ce Abubuwa Na Tafiya Dai-Dai A Najeriya

  • Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya ya ce ya kamata a duba kwakwalwar duk wanda ya ce abubuwa dai-dai suka tafiya a kasar
  • Tsohon shugaban kasar ya ce idan har ba a zabi shugabanni da suka cancanta ba a zaben shekarar 2023 kasar na iya rushewa
  • Obasanjo ya ce mutanen kasar ne kadai za su iya canja akalar kasar ta hanyar tabbatarwa sun zabi shugabanni da suka cancanta kuma masu kishin gina kasar a 2023

Jihar Legas - Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu Najeriya bata kai matsayin da ya kamata a ce ta kai ba.

A cewar Obasanjo, duk wanda ya ce abubuwa suna tafiya dai dai a kasar na bukatan a duba kwakwalwarsa, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Tagayyara Rayuwar 'Yan Najeriya, In Ji Tsohon Minista

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo
Obasanjo: A Duba Kwakwalwar Duk Wanda Ya Ce Abubuwa Na Tafiya Dai-Dai A Najeriya. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Obasanjo ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba wurin lakca na shekara-shekara ta Gidauniyar Badejo a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Najeriya bata kai matsayin da ya kamata ta kai ba. Duk wanda ya ce halin da muke ciki a kasar ba abin damuwa bane, ya kamata a duba kwakwalwarsa," in ji tsohon shugaban kasar.

A cewar Obasanjo, ya zama dole yan kasar su zabi dan takarar da ya dace idan ba haka ba kasar na iya rushewa, Daily Trust ta rahoto.

"Ko dai mu zabi wanda ya dace a 2023 saboda idan muka zabi wanda ya cancanta, za mu yi nasara," in ji shi.
"Amma, idan muka yi zaben tumin dare a 2023, abubuwa za su fi karfin mu kuma dole mu yi addu'ar kada hakan ya faru. Dole mu zabi wanda ya dace a 2023."

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

A watan Mayu, Obasanjo ya ce Najeriya na bukatar shugaba wanda ke kishin kasar da fatan ganin cigabanta.

Tsohon shugaban kasar ya ce halin da kasar ke ciki na 'wahalar' da shi da sauran yan Najeriya amma duk yadda abu suka kai, yan kasar ne kadai za su iya gyarawa.

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, A Yayin Da Farashin Kaya Ke Cigaba da Tashi A Kasar

A wani rahoton, tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Olusegun Obasanjo a ranar Talata 2 ga watan Agusta ya shiga jerin miliyoyin yan Najariya da ke kokawa kan tsadar rayuwa da wasu abubuwan.

Obasanjo ya bayyana cewa yana keta gumi sosai saboda tsadar dizal wanda ke shafar kasuwancinsa da wasu kasuwancin a sassan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164