Matan Da Suka Ki Amincewa Da Tayin Auren Maza Za Su Fara Biyan Tara A Chadi

Matan Da Suka Ki Amincewa Da Tayin Auren Maza Za Su Fara Biyan Tara A Chadi

  • Mutanen da suka ki yarda da tayin aure a Mangalmé da ke kasar Chadi dole ne daga yanzu su biya kudin tara
  • Sabuwar dokar ta ce mata da suka ki amincewa da tayin aure za su biya dala 23 da 39 yayin da maza za su biya dala 15
  • Kungiyar Musulunci ta jihar Mangalmé ce ta kafa wannan doka amma kungiyar kare yancin mata ta yi Allah wadai da ita

Wata sabuwar doka da aka kafa a wani bangare na Chadi ta ayyana cewa daga yanzu an wajabtawa matan da suka ki amsa tayin auren maza a jihar Mangalmé da ke arewa maso gabashin kasar biyan tarar dala 23 zuwa 39.

Sashin Hausa na BBC ya rahoto cewa kungiyar Musulunci ta jihar Mangalmé ce ta kafa wannan doka.

Kara karanta wannan

Yan Baiwa: Bidiyon Wasu Kyawawa Yan Gida Daya Da Duk Jikinsu Gashi Ne Har Fuska

Sai dai kuma, kungiyar kare yancin mata ta kasar Chadi ta yi watsi da wannan hukunci tana mai cewa ya saba ka’ida.

Yan mata
Matan Da Suka Ki Amincewa Da Tayin Auren Maza Za Su Fara Biyan Tara A Chadi Hoto: Channels tv
Asali: UGC

Hakazalika kungiyar kare yancin matan ta fara gangamin jan hankalin duniya zuwa ga wannan lamari a yanar gizo dauke da taken #stopAmchilini.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta yi hakan ne don nuna rashin amincewarta da wannan yunkuri na hukunta duk wanda ya ki amincewa da tayin aure.

Har ila yau, dokar ta shafi maza domin za su biya tarar dala 15 idan har suka ki yarda da tayin auren mace.

Kungiyar ta bayyana cewa lallai wannan sabuwar doka ta ci karo da dokar ba da yancin yanke shawara kan wanda mutum ke so ya aura.

BBC News ya kuma ruwaito cewa auren dole ya zama ruwan dare a kasar Chad, inda lamarin ya fi shafar kananan yara mata.

Kara karanta wannan

Bidiyon Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Magidanci Yayi wa Matashi Bayan Ya Ganshi Yana Tadin Mota da Budurwa

Duk da ayyana wata doka a 2015 wacce ta haramta yiwa kananan yara aure, amma kaso 60 cikin dari na mata masu shekaru daga 20 zuwa 24 an yi musu aure a lokacin su na yara bisa rahoton manazartar alkalluma da ke Chadi.

Yadda Budurwa Mai Shekaru 22 Ta Fada Soyayyar Tsohon Mai Shekaru 88 Har Ta Samu Juna Biyu

A wani labarin kuma, Chibalonza ta kasance matashiya yar shekaru 22, amma kuma sai ta fada a tarkon soyayya da tsohon da ya isa yin jika da ita, wato Kasher Alphonse mai shekaru 88.

Mutumin ya fada ma Afrimax English cewa sun kasance suna son juna kuma sun fahimci junansu duk da banbancin shekaru 66 da ke tsakaninsu.

A cewar masoyan wadanda suka shafe tsawon shekaru biyu tare, sun fada a tarkon soyayya da zuciyoyinsu ne amma ba wai da shekarunsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng