Ina son Ibo Su Daina Kiran Musulunci Addinin Hausawa Da Yarbawa – Mohammed Murtala Chukwuemeka

Ina son Ibo Su Daina Kiran Musulunci Addinin Hausawa Da Yarbawa – Mohammed Murtala Chukwuemeka

  • Mallam Mohammed Murtala Chukwuemeka ya zama abin burgewa bayan kaddamar da tarjamar kur’ani a harshen Igbo da ya fara shekaru biyar da suka gabata
  • Mallam Chukwuemeka ya ce ya kwashe shekaru biyu yana fassara suratul Bakara wanda ta ce sura mafi yawa da dadewa a cikin alkur'ani
  • Chukwuemeka Ya ce yana son Ibo su Fahimci cewa addinin musulunci na kowa da kowa ne

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Imo - Mallam Mohammed Murtala Chukwuemeka ya zama abin burgewa bayan kaddamar da tarjamar kur’ani a harshen Igbo da ya fara shekaru biyar da suka gabata. Rahoton BBC NEWS Pidgin

Dan asalin jihar Imo wanda ya musulunta shekaru 33 da suka gabata ya bayyana cewa ya fassara ayoyin kur’ani 6,236.

A wata hira da yayi da BBC News Pidgin, Chuwkuemeka ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda yana son 'yan kabilar Igbo su san addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Azabar Ta Yi Yawa: Ma’aurata Sun Maka Makwabcinsu Da Zakaransa A Kotu, Hotunan Sun Yadu

Alkuran
Ibo Suna Kiran Musulunci Addinin Hausawa Da Yarbawa – Inji Muslimin Da Ya Fassara Al-Qur'ani Zuwa Yaren Ibo FOTO BBC PIDGIN
Asali: UGC

Chuwkuemeka ya ce ya fassara kur’ani ne zuwa harshen Ibo saboda yana son ‘yan kabilar Igbo su san addinin Musulunci kamar yadda suke kiransa da addinin Hausa, Yarbawa da Larabawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace:

"Ba su yarda Musulunci na kowa da kowa ba ne. Akwai Kur’ani na Hausa, Kur’ani na Yarbawa, Kur’ani na Turanci, amma babu a yaren Igbo."

Chuwkwuemeka ya ce ya samu yabo da jinjina daga wurin Hausawa da Yarbawa fiye da yan kabilar sa na Ibo.

Chuwkuemeka ya kara da cewa wasu Hausawa da Yarbawa da suka karanta Kur’ani da ya fassara a harshen Igbo sun yi farin ciki sosai. Hakika sun ji dadin hakan fiye da ’yan kabilar Ibo na.

Yace:

"Wasu daga cikinsu ma sun ce za su yi amfani da kur’ani don koyon harshen Ibo."

Yayin da yake bayyana cewa Suratul Baqarah ita ce sura mafi tsawo a cikin Alkur’ani da ya fassara yace ya dauki shekara 2, Chukwuemeka ya yaba wa al’ummar Musulmi da suka taimaka masa wajen samun nasararsa.

Kara karanta wannan

Ta karewa PDP a Sokoto yayin da fitaccen kwamishina ya kaura, ya koma APC

Chuwkuemeka ya ce da al'ummar Musulmi ba su karbe shi a matsayin dan kabilar Ibo ba, da bai yi nasarar fasara tafsirin Al-Qur'ani ba.

Arzikin Aliko Dangote ya ragu zuwa dala biliyan 19, wanda yanzu ya zama na 80 mafi arziki a duniya

A wani labari kuma Legas - Aliko Dangote, wanda ya kafa kamfanin Dangote kuma attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyan Afirka, ya ga an daidaita kiyasin dukiyarsa yayin da ake sayar da hannun jari a Simintin Dangote.

A lokacin da aka kammala zaman ciniki na ranar Talata, arzikin dan kasuwar dan asalin jihar Kano ya dawo dala biliyan $19, wanda ya mayar da shi 80 a cikin jerin attajiran duniya da kididdigar Bloomberg ta fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa