An Tsinci Gawar Wani Mutumi da Wata Mace a Wani Kango Tsirara a Suleja

An Tsinci Gawar Wani Mutumi da Wata Mace a Wani Kango Tsirara a Suleja

  • Mutane sun tsinci gawarwakin wasu mutum biyu, namiji da mace tsirara a wani Kango a yankin karamar hukumar Suleja, jihar Neja
  • Mutumin da ya fara ganin gawarwakin ya bayyana yadda ya gan su yayin da yaje kusa da Kangon yin bayan gida
  • Wannan na zuwa ne yayin da mutane suka fara tashi daga wasu Anguwannin cikin Katsina saboda tsoron yan bindiga

Niger - An gano gawar Wani mutumi da aka gano sunasa, Adeyemi, da wata mata da ba'a san bayananta ba a wani gini da ba'a karisa ba a Anguwan Gwari, Kwanba a ƙaramar hukumar Suleja, jihar Neja.

Wani mazaunin yankin, Ikechukwu Michael, wanda ya fara ganin gawarwakin ranar Talata, ya bayyana cewa ya je kusa da Kangon da nufin yin bayan gida, sai ya ji wani wari na tsaro wa daga ciki.

Kara karanta wannan

Wasu Mutum Uku Sun Tsallake Rijiya da Baya a Hannun Mutane Bayan Asirin Su Ya Tonu a Abuja

Taswirar jihar Neja.
An Tsinci Gawar Wani Mutumi da Wata Mace a Wani Kango Tsirara a Suleja Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto a kalamansa Mista Michael ya ce:

"Na ga mutumin tsirara babu tufafi a jikinsa yayin da ita kuma budurwan na ganta rabin jiki tsirara. Tuni fatar gawar marigayi Adeyemi ta fara salewa. Ita macen na ganta kwance kan fuskarta, da ganin haka sai na ankarar da mutane."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa jim kaɗan bayan gano gawarwakin mutanen biyu, jami'an yan sanda suka iso wurin, suka kwashe su zuwa ɗakin aje gawarwaki.

Shin yan uwan mamatan basu neme su ba?

Wani wanda ya yi wa marigayi Adeyemi farin sani, Ogundipe Ayo, ya shaida wa wakilin jaridar cewa yayin da ya kira matar mamacin ta nuna masa bata san da faruwar lamarin ba.

A cewarsa, ta shaida masa cewa rabonta da Mai gida tun ranar Lahadi da yamma kuma idan ta neme shi bata samun shi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

Hukumar yan sanda reshen jihar Neja ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba a yanzu da muke kawo muku wannan rahoton.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun sake kai farmaki cikin birnin Katsina da sakar rana, Mutane sun tarwatse

Mutane sun tarwatse yayin da suka ga yan bindiga sun shigo Anguwannin su da tsakar rana a birnin Katsina, jihar shugaban ƙasa.

Wasu da abun ya faru a idon su sun bayyana cewa yan bindigan sun biyo ne yayin da suka taso wasu makiyaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262