Da Kaina Zan Zaba Miji In Darje: Budurwa Dake Sana'ar Hakar Burtsatsai

Da Kaina Zan Zaba Miji In Darje: Budurwa Dake Sana'ar Hakar Burtsatsai

  • A wani yanayin aiki wanda aka fi samun maza a ciki, wata budurwar Najeriya mai suna Maryam Hussain ta nuna cewa mace zata iya haka burtsatsai
  • Mai digirin a fannin fasahar katako, ta kwashe sama da shekaru goma tana aikin haka burtsatsai inda tace kwalliya na biyan kudin sabulu
  • Budurwar mai alfahari da aikinta, tace da kanta zata darzo mijin aure duk da yadda maza ke tururuwar a kanta, duk da a bayan tana ganin sana'arta zata kashe mata kasuwar maza

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Wata budurwa 'yan Najeriya mai suna Maryam Hussain, wacce ke haka burtsatsai a matsayin sana'a ta shawarci matasa da masu digiri da su kirkiri sana'a a maimakon jiran aikin gwamnati.

A tattaunawarta da BBC News Pidgin, zakakurar budurwar ta bayyana yadda ta fada aikin da aka san maza da shi. Maryam tace mutane na zundenta a lokacin da ta fara wannan sana'ar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Magidanci Yayi wa Matashi Bayan Ya Ganshi Yana Tadin Mota da Budurwa

Maryam Borehole
Da Kaina Zan Zaba Miji In Darje: Budurwa Dake Sana'ar Hakar Burtsatsai. Hoto daga BBC Pidgin
Asali: UGC

Yadda Maryam ta zama mai hakar burtsatsai

Maryam wacce ke da digiri a fannin fasahar katako, tace tuntuni ta so bude shagonta na kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma saboda rashin kudi da kuma irin gidan da ta fito, bata samu kudin yin hakan ba wanda yasa ta koma haka burtsatsai. Maryam tace ta kwashe sama da shekaru 10 tana haka burtsatsai a Kaduna.

Matashiyar budurwar tace lokacin da ta fara, ta dinga tsoron cewa maza ba za su so ta ba saboda irin sana'arta, amma hakan bata faru ba.

Maryam tace irin mazan dake kawo kansu wurinta ba mazan aure bane, matasa marasa mata ne ke zuwa.

Sai dai tace, da kanta zata zaba kuma ta darje irin mijin da zata aura.

Maryam tana jin kanta tamkar namiji idan tana aiki

Maryam ta tuna cewa, a lokacin da ta fara sana'arta, jama'a zundenta suke yi, amma yanzu kamar wata fitacciyar jaruma take jin kanta.

Kara karanta wannan

Wani Dan Najeriya Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Budurwar Sa Ta Nemi Auren Sa Da Kyautar Tsaleliyar Mota

A bangaren kalubalen da take fuskanta, mai haka burtsatsai tace mahaifinta ne matsalar farko.

"A lokacin da ba fara aiki,na fara samun matsala da mahaifinta saboda baya son sana'ar. Amma lokaci na tafiya, ya zo ya hakura saboda ya ga yadda nake taimakon kannaina dake makaranta da kudin da nake samu," tace.

Maryam ta bayyana cewa, har ofishin ta bude a gidan mahaifinta.

Soshiyal midiya sun yi martani

@almuhajiron yace: "Allah ya zaba miki miji nagari."
@rosy_kech tace: "Iyaye don Allah ku dinga bai wa 'ya'yanku kwarin guiwar da ta dace. Sannu da aiki sarauniyar."
@jasonfoodng tace: "Sannu da aiki yarinya. Kin yi nisa tuni, ina matukar alfahari da ke."
@ibom_princess tace: "Me ya dame su idan kin yi aikin maza? Cigaba da aikin ki. Idan miji ne, tsuguna ki zaba da kyau."
@meridian488: "Ubangiji zai cigaba da sanya miki albarka. Kada ku dogora da batun gwamnati, aiki tukuru yafi komai."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Budurwa Ta Gwangwaje Saurayinta da Kyautar PS5 Sabo Dal

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng