Tsohon Dan Majalisar Tarayya A Zamanin Mulkin Shagari, Alhaji Musa Tanko Abari, Ya Rasu
- Fittacen dan siyasar Najeriya kuma kwamishina a hukumar RMAFC, mai wakiltar birnin tarayya Abuja, Alhaji Musa Tanko Abari, ya rasu
- Abari, a cewar wani dan uwansa, ya rasu ne a ranar Talata 9 ga watan Agusta a wani asibiti mai zaman kansa, bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
- Rahotanni sun nuna cewa marigayin dan majalisar wakilai na tarayya ne a zaman mulkin tsohon shugaban kasa marigayi Shehu Shagari a 1981/82
Kwamishinan Hukumar Rarraba Haraji na RMAFC mai wakiltar birnin tarayya Abuja, FCT, Alhaji Musa Tanko Abari, ya rasu.
Wani dan uwan marigayin, Isiyaku Musa, wanda ya tabbatarwa Daily Trust rasuwar a wayar tarho, ya ce Abari ya rasu misalin karfe 2.34 na ranar Talata, bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja.
APC Ta Faɗi Sunan Wani Gwamnan PDP Dake da Hannu a Matsalar Tsaron Jiharsa, Ta Nemi a Kayar da Shi a 2023
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce marigayin ya fara rashin lafiya ne a makon da ya gabata kuma bai samu sauki ba har ranar Talata lokacin da rashin lafiyar ta kara zafi aka garzaya da shi asibiti.
An fara shirin jana'izarsa
Musa ya ce ana shirin daukan gawar mamacin daga asibitin zuwa kauyensu na Jiwa da ke Abuja Municipal don masa jan'iza.
Daily Trust ta gano cewa marigayi Abaji dan majalisar wakilai na tarayya ne a zamanin marigayi tsohon shugaban kasa Shehu Shagari a shekarar 1981/82.
Marigayin, wanda jigo ne a jam'iyyar APC a Abuja, ya yi takarar kujerar sanata na Abuja a tsohuwar jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC) a 2011 amma bai yi nasara ba.
Gogaggen Dan jarida, Mallam Abdulhamid Agaka Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
A wani rahoton, gogaggen dan jarida kuma kwararre a bangaren kafar watsa labarai, Mallam Abdulhamid Agaka, ya riga mu gidan gaskiya, rahoton Leadership.
A cewar kafar watsa labarai ta PRNigeria, dan jaridar wanda matarsa da mutu a makon da ya wuce, ya mutu cikin barcinsa a daren ranar Laraba a gidansa da ke Kaduna.
An haife shi a ranar 26 ga watan Fabrairun 1956, Malam Babatunde Agaka ya yi karatun frimare a Capital School Kaduna, kafin ya tafi Kwallejin Barewa da ke Zaria, duk a Kaduna ya kuma tafi Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Ilorin, Jihar Kwara.
Asali: Legit.ng