Daga Karshe, Shugaban APC Na Kasa Ya Yi Magana Kan Shirin Tsige Shugaba Buhari
- Shugaban APC, Abdullahi Adamu, ya ce yunkurin yan majalisar tarayya na tsige Buhari wani cigaba ne abun takaici da nadama
- Tsohon gwamnan jihar Nsarawan ya ce haka na faruwa a kowace kasa amma har waɗan da suka kirkiri lamarin sun gudu
- Adamu ya yaba da kokarin gwamnatin game da yajin aikin ASUU, ya nuna fatan ganin ɗalibai sun koma aji nan gaba kaɗan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana yunkurin tsige shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da wasu yan majalisa suka yi da wani lamari abun takaici.
Adamu ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da kafar talabijin ta Trust TV ranar Talata, 9 ga watan Agusta, 2022 a birnin tarayya Abuja.
Idan baku mance ba Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa yan majalisun tarayya sun yi barazanar fara bin matakan tsige shugaban ƙasa daga kujerarsa a wani taron manema labarai jim kaɗan kafin tafiyar su hutun watanni biyu.
Mambobin majalisar sun yanke wannan hukuncin ne bayan sun baiwa shugaban ƙasan wa'adin makonni Shida ya shawo kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake maida maryani kan batun, shugaban APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Adamu ya ce yunkurin babban abun takaici ne, "wanda ya bar kan turba mai kyau.'
A kalamansa ya ce:
"Shirin shige shugaban ƙasa babban abun takaici ne da babu shi kwata-kwata yanzu. Tare da majalisar tarayya, muna tsammanin irin haka, yana faruwa a ko ina a kowace demokaraɗiyya."
"A duk lokacin da ya zo kanka, ka cigaba da kokari, hatta waɗan da suka kirkiri yunkurin sun sauya daga kan hanyar."
Wane mataki APC take ɗauka na kawo karshen yajin aikin ASUU?
Da yake martani kan yajin aikin Malaman Jami'o'i da kokarin jam'iyya mai mulki na ganin ɗalibai sun koma azuzuwan su, Adamu ya ce APC ta yaba kwarai da yadda iyaye da ɗalibai ke nuna damuwar su.
Ya kuma yi fatan cewa ƙungiyar ASUU zata "dawo cikin hayyacinta a zahirance" ta dawo kan teburin sulhu.
"Ban sani ba kuma ina yaba wa da namijin kokarin da gwamnati ke yi, kana ina fatan ASUU zata dawo hayyacinta tare da gwamnati, ta haka kaɗai zamu cimma matsaya."
A wani labarin kuma Jerin jihohin Najeriya 20 da APC ka iya shan kaye saboda rikicin cikin gida a zaɓen 2023
Idan har ikirarin shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, cewa rikicin cikin gida ne ya jawo musu faɗuwa a zaɓen Osun , kuma ya kasance Mai ɗorewa, APC na fuskantar faruwar irin haka a jihohi 20.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Mafi yawan rassan jam'iyyar APC na jihohi sun shiga cikin rikici sakamakon saɓani ko kuma wani abu da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani.
Asali: Legit.ng