Rashin Tsaro: Za a Yi Zaben 2023, Shugaban Tsaro Ya Tabbatarwa 'Yan Najeriya
- Hafsan hafsohin tsaro ya bayyana cewa, Najeriya za ta shaida gudanar da zaben 2023 cikin lumana
- 'Yan Najeriya da dama sun nuna damuwa kan yiwuwar gudanar zaben 2023 ganin yadda kasar ke kara dagulewa
- An kama wasu da ake zargi da kai hari coci a watan Yunin da ta gabata, kamar yadda hafsan tsaron ya bayyana
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Yayin da ake ci gaba da ganin tabarbarewar tsaro a kasar nan, babban hafsan sojin kasa, Janar Lucky Irabor ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa za a gudanar da babban zaben 2023.
‘Yan Najeriya sun nuna damuwar ko za a yi zaben 2023 ganin yadda lamurran tsaro da karuwar hare-haren 'yan ta'adda ke kara ta'azzara.
Sai dai, da yake magana a yayin wani taron manema labarai a ranar Talata a hedkwatar tsaro da ke Abuja, Janar Irabor ya ce sojoji za su yi duk mai yiwuwa don ganin cewa babu abin da ya hana gudanar da zaben.
Babban hafsan tsaron ya kuma nanata kudurin sojojin Najeriya na kare manufofin dimokaradiyya a kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa, sojoji sun yi alkawarin kare dimokuradiyyar Najeriya kuma ba za su canza daga matsayin ba.
An yi taron ne domin neman goyon bayan kungiyoyin yada labarai don tunkarar kalubalen tsaro a kasar, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.
Wannan dai shi ne karo na biyu a jerin tattaunawa tsakanin babban hafsan hafsoshin tsaron kasar da shugabannin zartarwa da editocin kungiyoyin yada labarai a Najeriya.
A baya dai haka mai ba shugaban kasa shawari ya bayyana, cewa za a yi zaben 2023 cikin lumana sabida shirin da ake yi, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ya kuma yi amfani da damar wajen bayyana cewa an kama wadanda ake zargin suna da alaka da wani harin ta’addanci da aka kai a cocin Saint Francis Catholic da ke Owo watanni biyu da suka gabata.
Da zafi-zafi: Sojoji sun gano dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura, sun sheke shi
Ko da yake bai bayyana adadin wadanda ake zargin ba, Irabor ya bayyana cewa an kama maharan ne a yayin wani samame na hadin gwiwa da ya hada da rundunar soji da jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da kuma ‘yan sanda.
Kimanin mutane 40 ne suka mutu a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari cocin a ranar 5 ga watan Yuni, inda suka bude wuta kan masu ibada.
Zabe za a yi ba 'wuruwuru': Shirin da Buhari ke yi gabanin babban zaben 2023
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa ba zai bari a yi magudin zabe ko rashin da’a a karkashin kulawarsa ba a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban ya fadi haka ne a wani taron karawa juna sani kan harkokin tsaro na ‘Election Security Management’ wanda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta shirya a Abuja.
Shugaban ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), inda ya ba da tabbacin cewa babu wata jam’iyyar siyasa ko wani mutum da zai zo da wargi a lokacin zabe.
Asali: Legit.ng